Yau Lahadi 21 ga watan Satumba manyan kungiyoyin kwallon kafa biyu – Arsenal da Manchester City za su buga wasan zagaye na 5 na gasar Firimiya ta bana da misalin karfe 4:30 ns yamma a filin wasa na Emirates da ke birnin Landan.
Arsenal wadda a yanzu haka ta ke matsayi na 3 da maki 9 a wasanni 4 da ta buga, za ta karbi bakuncin Manchester City wadda ke matsayi na 12 da maki 6 bayan wasanni 4, wasa tsakanin kungiyoyin biyu na daga cikin wasanni masu matukar burge masu sha’awar kallon kwallon kafa a Duniya sakamakon yadda Giwayen biyu ke nuna kwarewa da jajircewa a duk lokacin da suka hadu a filin wasa.
Kungiyoyin biyu sun hadu da juna sau 214 a tarihi, Arsenal ce ke kan gaba wajen samun nasara inda ta doke City sau 100 aka buga canjaras 48 yayinda City ta doke Arsenal sau 66, wannan wasan na yau shi ne karo na 11 da Arteta zai fuskanci tsohon maigidanshi a matsayin kocin Arsenal.
Yayin da Arsenal ke neman lashe gasar Firimiya karo na farko cikin shekaru 20, hakazalika Manchester City na fatan ganin ta dawo cikin hayyacinta bayan rashin nasara a wasanni biyu a jere da tayi a farkon wannan kakar ta bana.