Lamarin da aka sa gaba kan ilimi
Ana kara inganta yadda ake koyar da ilimi saboda a samu biyan bukatun abubuwan da zasu kasance suna tafiya daidai da yadda duniya take.Abubuwan da za a tafiya da su in hakan ta taso sun hada da:
Samar da ilimi domin bukatu daban daban
Koyo: Koyar da ilimi ga yadda ya bukaci bukatun kowa, manufa yadda za a bar dalibai su rika samun ci gaba daidai lokacin da suka bukata,da kuma suke so.
Mai da hankali sosai kan koyo (CBE):Yadda za a tabbatar da dalibai sun fahimci abinda ake kowa masu da gane shi sosai tare da dukkan dabarun ko hikimomin kafin nsu kai ga zuwa ga zuwa bangare nag aba da kuma fahimtar dukkan darussan.
Mai da hankali sosai kan dabaru:Kara bada muhimmanci ga yadda za a inganta mu’amala da tuntuba tsakanin juna,hada kai domin ayi aiki tare, da kuma maganin matsala lamarin da shi ne ginshikin yadda ma’aikata za su cimma burinsu.
Lamarin kimiyya,fasaha,da kuma ilimin injiniya (STEM) Yadda za a shirya ko tsara dalibai yadda zasu cimma burin abinda suke son su zama a gaba,manufa ayyukan da suke son yi,ko sun shafi kimiyya,fasaha,ko kuma abinda ya shafi injiniya ne da lisssafi,domin wadannan lamurran wasu bangarori ne da suke samr da ci gaan tattalin arziki
Dabarun koyarwa:Wadanda suka hada da hanyar gargajiya da kuma,ta kafafen sadarwa na zamani,domin kuwa hakan ne kadai zai iya samar da hanyoyi ko dabarun koyarwa.
Lamarin lafiyar da ya maida hankali kan abubuwa:Mai da hankaliko kuma tabbatar da dukkannin abubuwan da aka san ko tabbatar da cewar za su bada
Cikakkiyar, gudunmawa ga su dalibai masu koyo,abin ya kasance daga karshe yayi kyau.
Damar da ake samu a duniya ta harkar ilimi:Ilimi yana samar da dama ta gane/ fahimtar lamurran duniya ta hanyoyin yin wasu ayyuka.
Hanyar da za’a cigaba da koyo: Bada dama wadda za a ci gaba da koyon dabaru amma fa ta hanyoyin da suka dace da kuma kamata.
Manhajar zamani dake taimakawa wajen koyon ilimi ko kuma karatu (AI): Samar da hanyoyin da ake koyar da wadanda suke koyo wasu abubuwan da suka shafi harkar ilimi.
Ilimin maida hankali domin shiryawa lamarin gaba: Mai da hankali kan al’amarin daya shafi muhalli da wasu abubuwan da zasu taimakawa dalibai fuskantar matsalolin duniya.
Irin wadannan harkokin sun nuna bukatar da a koma tsarin da zai iya tafiya da zamani lamarin da zai shirya dalibai su ma su yi shirin fuskantar lamurran duniya nan gaba.
Ta yaya tsarin ilimin da ba zuwa makaranta ake ba yake taimakawa samun bunkasa a wajen aiki?
Ilimi na wata manufa daban wadda ta sha bambanci da yadda ake zuwa makaranta,ana tsara abin ne ga dalibai wadanda ba za su iya zuwa makaranta bako kuma wadanda bukatar ta koya masu ta musammance.Irin wannan tana samar da wata hanya ta koyarwa da zata biya bukatun da su masu koyon,ko ake koya masu suke dasu.
Yanzu a kasuwar neman aiki ta duniya,ilimin da ya sha bamban da wanda ake yi a makaranta yake maganin bukatun irin wadanda suke bukata ta hanyar ilimi da ake samrwa wanda ba sai anje,makaranta baIrin wadannan tsare tsaren sun,hada da kwasa kwasai da kuma digiri irin wadanda ke sa wadanda basu samu damar zuwa makaranta,ba suke ko ake amfani da shi yadda zasu samu dabaru ko kwarewa wadanda za su taimaka,masu kamar wadanda suka samu damar zuwa makarantar.Irin wadannan kokarin wata hanya ce,wadda ake gwada takardun sheda na ilimi da aka samu a makaranta da kuma irin tsarin daya sha bamban da shi.Alal misali kwararru wadanda suke bukatar dasu kai cimma burin su na sha’anin daya shafi kula da lafiya,suna iya amfani da tsarin kafar sadarwa ta zamani kai tsaye ta hanyar amfani da tsarin MSN na wadanda ba suyi kawas din Nas- Nas ba,wanda irin tsarin ne kuma ake sa ran zai iya maganin tsaikon da ake da shi tsakanin wadanda suka je makaranta suka samu horo,wajen abubuwan da ake bukatar su kwararru ta bangaren kwas din Nas,su samu.
Yanzu ne ya dace a kawo gyara akan lamarin ilimi
Yin wata dawainiya ko zuba jari a harkar ilimi daga karshe ko bad ade- ko ba jima hakan yana taimakawa, duk da yake dai abin yana dauykar lokaci kafin a kai ga cimma buri. Yana daukar lokaci mai matukar tsawo kafin,an cimma burin hidimar da aka yi dangane da lamarin ilimi, wato kamar Malaman makaranta, yadda ake amfani da fasaha kamar yadda ya dace,da kuma shi tsarin na ilimi. Sai dai kuma.Tarihi ya nuna kasashe wadanda suke samun ci gaban da ake bukata duk sun dauki matakin daya dace ne, dangane da ilimi bada was aba ko suka yi ma shi rikon sakainar kashi.(Bankin Duniya,2019)
Wani abu kuma daban shi ne wadanda basu kammala makaranta ba suna raguwa,amma kuma kudaden da suke shiga hannun mutane sune suka ragu.Ya kamata matasa su ci gaba da koyon neman ilimi domin su kasance daidai da yadda lamurran duniya suke sauyawa a tattalin arziki wanda ake ta gogaiya,ga kuma yadda canza shi fasalin aikin yi da wadanda ya dace su kasance ma’aikata wadanda su kan kasance wadanda ake ta rubibin su.Don haka wannan ne lokacin da za ayi gyara,kan harkar ilimi,wannan kuma sai fa idan har al’umma suna bukatar su amfana da abubuwan da za su biyo bayan daukar mata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp