Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), Farfesa Adamu Ahmed, ya ce jami’ar na kashe sama da Naira biliyan huɗu duk shekara wajen samar da wutar lantarki, abin da ya bayyana a matsayin abu da ba zai ɗore ba.
Yayin bikin cika shekaru 63 da kafa jami’ar, Farfesa Ahmed ya ce gwamnati ta bayar da Naira biliyan ɗaya ta hannun TETFund domin tallafa wa jami’ar, tare da amincewa da sabon aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai ƙarfin megawat 10.
- Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa
Ya ƙara da cewa tsoffin ɗalibai na jami’ar sun haɗa kai da shugabancinta wajen samar da makamashi mai ɗorewa, musamman ta hanyar amfani da hasken rana.
Jami’ar ABU, wadda aka kafa a 1962, ta kasance ɗaya daga cikin manyan jami’o’in gwamnati a Nijeriya a shekarar 2025, kuma tana cikin manyan jami’o’i uku da suka fi daraja a ƙasar.
Farfesan, ya kuma bayyana cewa jami’ar na ƙoƙarin bunƙasa tsaro ta hanyar aiki tare da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin mutane a ciki da wajen jami’ar.