Peter Rufa’i, daya daga cikin fitattun masu tsaron raga na tawagar Super Eagles ta Nijeriya, kuma fitaccen dan wasan kwallon kafa na Afirka, ya rasu a ranar Alhamis, 3 ga watan Yuli, 2025, ya bar tarihi da ke ci gaba da zaburar da ‘yan wasan kwallon kafa da masoya.
Jajircewa da jagoranci, na daga cikin halayen da Rufai ya bari a cikin zukatan wadanda suka yi rayuwar kwallo tare da shi, da kuma dubban ‘yan Nijeriya masu sha’awar kwallon kafa da suka samu damar kallon wasanninsa a lokacin da yake sanye da riga mai tambarin shaho kuma yake tsaye a bakin ragar Nijeriya domin tare duk wani hari irin na wannan wasa ta kwallo mai miliyoyin masoya a fadin duniya, “Dodo Mayana”, kamar yadda ake kiran sa ya kasance babban jigo a fagen kwallon kafa a Nijeriya.
- Dan Gidan Ancelloti Ya Zama Sabon Kocin Botafago FC
- NAFDAC Da Masu Maganin Gargajiya Za Su Tsabtace Sana’ar Sayar Da Maganin Gargajiya A Nijeriya
Bayan gudummawar da ya bayar a filin wasa, rayuwar Rufa’i ta kasance wani nau’i na musamman na da ke dauke da juriya, sadaukarwa, da sha’awar wasan.
A yayin da ‘yan Nijeriya da ma duniyar kwallon kafa ke juyayin rashin sa, ga abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da marigayi golan Super Eagles.
1. Peter Rufa’i Ya Fito Daga Gidan Sarauta
An haifi Peter Rufa’i a ranar 24 ga watan Agusta, 1963, a Oshodi, Legas, a wani gidan sarautar gargajiya, Mahaifinsa shi ne sarkin kabilar Idimu a Jihar Legas, duk da hasashen da ake yi na cewa zai yi gadon sarautar gidansu, Rufa’i ya yi watsi da sarautar don ci gaba da fuskantar abin da yake sha’awa wato kwallon kafa.
2. Ya yi Wasa A Manyan Kungiyoyin Kwallon Kafa A Kasashen Turai
Rufa’i ya fara sana’ar kwallon kafa a kungiyoyin gida Nijeriya kamar Storeery Stores da Femo Scorpions kafin ya tsallaka zuwa kasar waje, ya taka leda a kungiyoyi a kasar Benin (Dragons de l’Ouémé), Belgium (Lokeren, Beberen), Netherlands (Go Ahead Eagles), Portugal (Farense, Gil Bicente), da Spain (Hércules, Deportibo La Coruña), inda ya samu gogewa a bangaren da yake na mai tsaron raga.
3. Ya Taimakawa SC Farense Wajen Samun Damar Buga Kofin Turai (UEFA)
A lokacin kakar shekarar 1994–95, Rufa’i ya taka rawar gani wajen taimaka wa kulob din SC Farense na Portugal samun nasarar shiga gasar cin kofin UEFA na farko, ya ci gaba da zama a kungiyar inda aka zura masa kwallaye 38 kacal a wasanni 34 da ya buga a wannan kakar wasan.
4. Shine Mai tsaron Ragar Nijeriya Na Farko A Gasar Kofin Duniya
Rufa’i ya buga wa Nijeriya wasanni 65 na kasa da kasa, kuma shi ne mai tsaron raga na farko da Nijeriya ta zaba a gasar cin kofin duniya na FIFA a shekarun 1994 da 1998, ya kuma taka muhimmiyar rawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Nijeriya ta yi a kasar Tunisia a shekarar 1994.
5. Ya Taba Ci Wa Nijeriya Kwallo
Yayin da ba kasafai ake samun mai tsaron raga ya ci kwallo a wasan kwallon kafa ba, Rufa’i ya zura wa Nijeriya kwallo a bugun fenareti a wasan da suka doke Habasha (Ethiopia) da ci 6-0 a wasannin neman gurbin shiga gasar AFCON a shekarar 1993, ita ce kadai kwallon da ya taba ci wa Nijeriya, kuma ta kasance daya daga cikin lokutan da ba zai taba mantawa da shi ba a rayuwarsa.
6. Ana Yi Masa Lakabi Da “Dodo Mayana”
Masoya nayi wa Rufa’i lakabi da “Dodo Mayana” saboda zafin nama da yadda yake tare kwallaye cikin kwarewa, lakabin ya zama tamkar wani kamanceceniya da yake yi da Dodo na asali duba da yadda yake yin abin da ba ayi tsammanin cewa zai iya yi ba.
7. Ya Yi Makarantar Aikin Horarwa Domin Samun Lasisin Horarwa
Bayan ya yi ritaya daga buga kwallon kafa, Rufa’i ya dawo aji a shekarar 2023, inda ya shiga Cibiyar kula da wasanni ta kasa da ke Legas don samun takardar cancantar zama koci, yana daga cikin babban kokarin da ya yi wajen ganin ya ci gaba da taimaka wa matasa masu tasowa wajen kwarewa da jagoranci a harkar kwallon kafa.
8. Ya Kafa Makarantar Kwallon Kafa ta Staruf
Mai himma wajen bunkasa matasa, Rufa’i ya kafa makarantar horar da kwallon kafa ta Staruf a Legas, har ila yau, ya kasance mai bayar da shawara akan a saka wasanni cikin jadawalin koyarwa a Nijeriya, ya kuma bukaci iyaye a Nijeriya da su yi kokarin cikar burin ‘ya’yansu na zama cikakkun yan kwallo tare da karatun Boko a lokaci guda.
9. Yana Da Matukar Jajircewa Akan Abin Da Ya Saka A Gaba
Rufa’i ya bayyana cewar tsawon shekaru 20 fa ya shafe a matsayin dan kwallon kafa bai rasa nasaba da yadda yake da jajircewa a duk abin da ya saka a gaba, inda yake cewa ina bayar da himma fiye da kashi 100 a koda yaushe, wadannan dabi’un, in ji shi, sun taimaka masa ya yi nasara a kasashe da dama da kuma fuskantar matsin lamba.
10. Yaba Karbar Laifinsa Idan Akayi Rashin Nasara
Duk da rawar da ya taka a fagen kwallon kafa a tsawon lokaci, rashin nasarar da Nijeriya tayi a hannun Denmark da ci 4-1 a gasar cin kofin duniya na shekarar 1998 a zagaye na 16 na daya daga cikin mafi munin wasannin da Rufa’i ya buga, ya bayyana shi a matsayin wasan da ya fi zafi a
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp