1- Kari wani dunkulallen bulli ne mai dan taushi ko tauri da kan fito a sassan jiki. Daga cikin ire-iren karin da ke fitowa a sassan jiki, akwai wani kari da ake kira da ‘ganglion cyst’ a turance. Irin wannan kari, yawanci ya fi fitowa ne a kan gaba.
2- Girman kari, kan kasance kamar girman kwayar wake zuwa girman kwayar gurjiya. Sannan, yanayinsa idan aka taba ko aka latsa shi yana kama da balan-balan ko ‘yar mitsitsiyar kwallo cike da ruwa mai kauri. A dunkule dai, wannan kari bulli ne da ke dauke da wani ruwa mai yauki da kuma kauri a ciki.
- Xi: Ya Kamata A Hada Hannu Domin Tafiyar Da Tattalin Arzikin Duniya Bisa Adalci Da Daidaito
- CMG Da El Comercio Group Na Kasar Peru Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zurfafa Hadin Gwiwa
3- Abin farin ciki shi ne, wannan kari ba kansa ko daji ba ne. Don haka, babu fargabar cewa zai iya fantsama zuwa sassan jiki ko kuma ya tilasta yanke hannun.
4- Kashi tamanin da takwas cikin dari (88%) na wannan kari, na fitowa ne a kan gabar tsintsiyar hannu; kashi goma sha daya cikin dari (11%) kuma, yana fitowa ne a gabobin tafin sawu da idon sawu.
5- Har ila yau, kowa zai iya samun wannan kari, sai dai mata sun ninka maza sau uku wajen samun karin tsintsiyar hannu. Sannan kuma, kashi saba’in cikin dari (70%); yana faruwa ne tsakanin shekara 20 zuwa 40 na rayuwa.
6- Kashi sittin zuwa saba’in cikin dari (60 – 70%) na karin tsintsiyar hannu, na fitowa ne a bayan tsintsiyar hannu. Inda sauran kason kuma ke fitowa a gaban ko gefen tsintsiyar hannun.
7- Mene ke kawo wannan kari? Babu wani takamaiman sababi da ke kawo wannan kari. Sai dai, ana ganin bugu, kabar majinar gaba, tunzuri ga majina ko tantanin gaba; sakamakon ayyukan da ke bukatar maimaituwar motsin gabar tsintsiyar hannun na kara hadarin faruwarsa.
8- Alamomin karin tsintsiyar hannu: Daga cikin alamomin karin tsintsiyar hannu akwai:
i- Bayyanar bulli ko tudun karin; idan aka lankwashe gabar tsintsiyar hannu. Kuma karin a wuri guda yake, ba yawo yake yi ba.
- Karin yana girma ne kadan-kadan, zai iya bullowa kwatsam! A wani lokaci kuma, sai ya kankance ko ma ya bace bat. Haka kuma, zai iya dawowa a kowane irin lokaci.
iii. Mafi yawan lokaci, karin tsintsiyar hannu; ba ya yin ciwo, sannan kuma ba shi da wata matsala. Amma ya kan fara yin ciwo ne, idan karin ya fara shake ko danne jijiyar laka a hanyarta ta zuwa hannu. Haka nan, yayin da karin ya danne jijiyar laka; zai iya haifar da ciwo, zugi, rauni ko rashin kwarin wani yatsa ko yatsun hannu.
9- Yaushe ya kamata a tuntubi likita? Za a iya tuntubar likita ne da zarar karin ya fara haifar da alamun da muka ambata a sama, domin bin hanyoyin magance karin da suka hada da; zuke ruwan cikin karin tare da sanya maganin da zai kafar da ruwan karin. Haka nan, ana yin tiyata don cire karin daga tushensa da sauran hanyoyi.
Bugu da kari, likitocin fisiyo na taka rawar gani kafin da kuma bayan tiyatar; wajen magance matsalolin ciwo, raunin ko rashin kwarin yatsu ko hannu da kuma magance matsalar tabon tiyata da sauran makamantansu.
10- Har wa yau, imma karin ba ya ciwo amma ka damu da munin sifar da karin ya jawo maka; to kana iya zuwa asibiti domin a cire maka shi.