Shugaba Bola Tinubu ya bayyana wasu muhimman abubuwa guda biyar da gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai.
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a jawabinsa na rantsar wa a matsayin shugaban Nijeriya na 16.
A cewarsa, babbar manufarsa itace, ci gaba da gudanar da shugabanci nagari don ciyar da manufofin Nijeriya gaba.
Ya ce, “Za a gudanar da mulkin Nijeriya ba tare da nuna son kai ba kamar yadda kundin tsarin mulki da tsarin doka ya tanada.
“Za mu kare al’ummar kasar daga ta’addanci da duk wani nau’in ta’addanci da ke barazana ga zaman lafiyar kasarmu da yankinmu.
“Za mu sake fasalin tattalin arzikinmu don samar da ci gaba da bunkasa ta hanyar samar da ayyukan yi, samar da abinci da kuma kawo karshen mugun talauci.
“A gwamnatinmu, mata da yara za su samu kaso mai yawa.
“Gwamnatinmu za ta ci gaba da daukar matakai masu inganci kamar dakile cin hanci da rashawa tare da karfafa hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa.”