“Ban mai da hankali sosai a kan matsalolin da makafi ka iya fuskanta a lokacin da suka fita ba, ina zaton watakila akwai matsalar mamaye hanyoyin musamman da aka gina musu da motoci suka yi, ko kuma hanyoyin sun lalace.”
“Ana samun hanyoyin musamman da aka ginawa makafi a birnin Beijing, a kantuna da sauransu duk akwai.”
“Ina ganin ya kamata a kara fadakar da al’umma, musamman ma yara, baya ga hakikanan matakan da ya kamata a dauka.”
“Ko a ban daki ma akwai hanyoyin musamman da aka ginawa masu bukata ta musamman, gwamnati na mai da muhimmanci sosai a kan wannan batu, tare da nuna kulawa sosai ga masu bukata ta musamman, wannan abin yabawa ne.”
Yadda aka mayar da amsa ke nan a yayin da muka tattauna da wasu mazauna birnin Beijing a kan titi game da batun kawar da matsalolin da masu bukata ta musamman ke fuskanta, wadanda suke ganin cewa, cikin ’yan shekarun baya, an samu ci gaba wajen magance matsalolin da masu bukata na musamman ke fuskanta, sai dai akwai bukatar kara daukar matakai.
Mr. Liu Weichang, dan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya yi na’am da kalaman da mazauna birnin suka yi.
Liu Weichang yana da nakassa a kafarsa sakamakon ciwon da ya ji a lokacin da yake karami. Ya ce a garinsu Handan dake da nisan fiye da kilomita 400 daga Beijing, akwai sauran aiki wajen magance matsalolin da masu bukata ta musamman ke fama da su. Ya ce, “Aikin kawar da matsaloli ga masu bukata ta musamman ya shafi mutane irina dake da nakassa. Yanzu aikin ya samu ci gaba sosai a manyan birane, amma a wasu kananan garuruwa, idan ba a gudanar da wannan aiki sosai ba, hakika ko zuwa ban daki ma na da wahala gare mu.
Abubuwan da ake ganin ba su da muhimmanci su kan zamo mana masu muhimmanci.”
Kamar yadda Liu Weichang ya fada, abubuwan da ba su da muhimmanci ga mutanen da ba su da nakassa, su kan zamo wa nakasassu masu muhimmanci. Don haka, aikin kawar da matsaloli ga masu bukata ta musamman na shafar moriyar mutane miliyan 85 da suke fama da nakassar wasu sassan jiki a kasar Sin.
A game da wannan, Cao Jun, shugaban kungiyar masu bukata ta musamman ta unguwar Chaoyang ta birnin Beijing, ya ba mu misali cewa, “Akwai bambancin fahimtar aikin kawar da matsaloli ga nakasassu a tsakaninmu masu bukata ta musamman da sauran al’umma. Al’umma kan mai da hankali a kan ko an mamaye hanyoyin musamman da aka gina wa nakasassu, amma abin da muka fi mai da hankali shi ne ko akwai hanyoyin musamman da aka gina mana a unguwarmu, ko zan iya fita yawo a unguwar ba tare da wata matsala ba, sa’an nan ko akwai sautin sanar da mu benen da muka isa a cikin na’urar hawan bene, in ba haka ba, za mu samu matsala.”
Ta yaya za a mai da wadannan hanyoyi da na’urorin hawa bene su rika biyan bukatun nakasassu, kuma a sa al’umma da kamfanoni da ma gwamnati su kara mai da hankali wajen saukakawa masu bukata ta musamman a yayin da ake gine-gine, suna jawo hankalin mahalarta taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wadanda suka gabatar da shawarwari da yawa dangane da magance matsalolin da masu bukata ta musamman ke fuskanta.
Madam Yang Jia, ta shafe tsawon shekaru 15 tana zama ’yar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, cikin shawarwari sama da 60 da ta gabatar, akwai da dama dake shafar kare hakkin nakasassu, wadanda gwamnati ta dauka. Tana ganin cewa, aikin kawar da matsaloli ga masu bukata ta musamman zai kuma amfani al’umma baki daya. Ta ce, “Aikin kawar da matsaloli ga masu bukata ta musamman zai kara samar da saukin rayuwa ga dukkanin al’umma, maza da mata, tsoffi da yara.”
Tare da ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma, cikin ’yan shekarun baya, ’yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa da dama sun sha gabatar da shawarwari na fadada aikin kawar da matsaloli ga masu bukata ta musamman, wato baya ga fannonin da aka saba, misali gina hanyoyi na musamman, ya kamata a mai da hankali a kan kawar musu da matsaloli a fannonin yawon shakatawa da kiwon lafiya da sauransu.
A wannan shekara, wasu mata ’yan majalisar uku sun gabatar da shawarar watsa fina-finai da masu fama da matsalar gani ma suke iya kallo a gidajen sinima a kai a kai, don masu fama da matsalar gani ma suke iya jin dadin wasannin kwaikwayo ta yin amfani da fasahohin zamani.
Cao Jun ya gamu da matsalar makanta tun da aka haife shi, don haka, ya fahimci matsalar da makafi ke fuskanta, musamman ta fannin samun saukin rayuwa ta yin amfani da fasahohin zamani. Don haka, a shekarar 2013, ya fara nazarin manhajar da za ta iya taimakawa masu fama da matsalar gani yin amfani da wayoyin salula, manhajar da daga baya ta samu matukar karbuwa. Ya ce, “Ta yaya makafi za su iya yin amfani da wayoyin salula? Ya kamata mu magance matsalar yadda makafi za su rika amfani da wayoyi na zamani, ta yadda wayar za ta rika karanta musu sakonni idan suka taba. Ta haka ne muka tsara manhajar.”
Kasar Sin na dora muhimmanci sosai a kan kare hakkin masu bukata ta musamman. A shekarar 1991, kasar Sin ta fara aiwatar da dokar kare hakkin nakasassu. A shekarar 2012, kasar ta kaddamar da dokar magance matsalolin masu bukata ta musamman, a kokarin saukaka musu yayin da ake gina ababen more rayuwa a cikin birane.
A wannan shekara, an fitar da karin ka’idoji game da aikin kawar da matsaloli ga masu bukata ta musamman a birnin Beijing da ma lardin Jiangsu, ciki har da kirkiro kayayyakin fasahohin zamani na tallafawa aikin kawar da matsaloli ga masu bukata ta musamman, musamman ta fannin yin amfani da yanar gizo.
Yadda aka gudanar da gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin hunturu a farkon bana a Beijing, shi ma ya taimaka wajen fahimtar da al’umma a kan muhimmancin aikin kawar da matsaloli ga nakasassu. Cao Jun ya samu damar halartar bikin bude gasar, kuma ya ce, “Mun zauna a wajen, kuma gaskiya abin ya burge mu matuka. Shugaban kasarmu Xi Jinping ya sanar da bude gasar, duk da cewa yana fama da aiki, amma ya zo wajen bikin bude gasar Olympics, haka kuma ya zo wajen bikin bude gasar Olympics ta nakasassu, lamarin da ya shaida cewa, muna zaman daidaito da wadanda ba su da nakassa, dukkanmu daya ne a idon shugaban kasarmu.”
Sai dai akwai bukatar kara kokari wajen kara fadakar da al’umma a kan aikin kawar da matsaloli ga masu bukata ta musamman. Madam Ping Yali, ’yar kasar Sin ta farko da ta lashe lambar zinari a gasar wasannin Olympics ta nakasassu, ta ce yana da muhimmanci a fara da fadakar da yara. Ta ce, “Akwai sansanin horar da karnukan dake yi wa makafi jagora, kuma kowane gida na da damar renon dan karamin kare, da yara da iyayensu tare.
Bayan shekara guda, za a fara yawo da karen da ake reno, a lokacin, yara za su iya sa masa suna na yi wa makafi fatan alheri, misali akwai sunan haske, akwai kuma rana, da zarar yara sun girma, za su san yadda za su kula da masu fama da matsalar gani.”
(Lubabatu Lei)