Allah tabaraka wa ta’ala ya fada cikin Annabi Ayyuba (AS), “madalla da bawan nan namu, shi mai yawan komowa wurinmu ne”, ya fada cikin hakkin Annabi Yahya da cewa, “Ya Yahya, ka rike Attaura da karfi, mun ba shi Annabta tun yana yaro, shi kuma rahma ne daga gurinmu, kuma sadaka ne ga halitta, mai tsoron Allah ne. mai bin Iyayensa ne, bai kuma zama azzalumi ba mai sabo. Amincin Allah ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi da ranar da zai mutu da ranar da za a tashe shi, ranar tsayuwa” – kadan daga cikin rahma daya tak ta Annabi (SAW).
Ubangiji tabaraka wa ta’ala ya fada cikin hakkin Annabi Zakariyya, “Lallai Allah yana maka bushara da Annabi Yahya, mai gasgata Kalmar Allah ne, shugaba ne kuma katangagge ne daga mata, Annabi ne daga cikin Annabawa”.
- Sojoji Sun Kashe Kasurgumin Kwamandan ‘Yan Bindiga A Kebbi
- Sabon Karatu: Tsantseni Da Gudun Duniya Na Annabi (SAW)
Ubangiji ya kara fada cikin hakkin Annabi Adamu da Nuhu da dangin Annabi Ibrahim (AS), “Lallai Allah ya zabi Annabi Adamu da Nuhu da ‘ya’yan gidan Annabi Ibrahima a bisa halitta, dangi ne sashi bayan sashi, Allah mai ji ne kuma masani ne”.
Ya kara fada cikin hakkin Annabi Nuhu, “lallai ya kasance bawa ne mai godiya”. A cikin hakkin Sayyada Maryam, Ubangiji ya fada da cewa, “Allah yana miki buhshara da kalma daga gare shi, sunan shi, ‘Masihu’ (wanda in ya shafa ake albarka ko kuma wanda aka shafa da albarka), mai alfarma ne a duniya da lahira, yana daga cikin makusanta, kuma zai yi magana da mutane yana cikin tsumman jego – a zamaninsa, zai yi magana da mutane yana a gwarzontaka – bayan ya dawo a wani zamani, yana daga cikin Annabawa.” Annabi Isah yana cewa, “lallai ni bawan Allah ne da Allah ya ba ni Littafi ya sanya ni Annabi, ya sanya ni mai albarka a duk inda na sauka sai wurin ya yi albarka, ya yi min wasiyya da yin Sallah da yin Zakkah matukar ina numfashi, kuma ya umurce ni da yin biyayya ga mahaifiyata, kuma bai sanya ni mai tsaurin kai ba kuma shakiyyi.”
Allah yake fada wa Sahabban Annabi (SAW), “ya ku wadanda kuka yi Imani, kar ku dinga fada wa Annabi (SAW) maganar da za ta bata masa rai, kar ku zama irin mutanen da suka cutar da Annabi Musa, sai Allah ya kubutar da Annabi Musa da abin da suka fada, Annabi Musa mai alfarma ne wajen Allah.” Manzon Allah (SAW) yake cewa, “Annabi Musa ya kasance mutum ne mai yawan kunya mai yawan suturce jikinsa, ba a iya ganin komai na jikinsa.”
Allah ya fada cikin hakkin Annabi Musa, “yayin da na gudu daga gare ku, sai Allah ya ba ni Hikima kuma ya sanya ni daga cikin Annabawa.”
Allah ya fada a cikin hakkin tulin Annabawa, “lallai ni a gare ku, manzo ne amintacce – kowane Annabi haka yake fada wa al’ummarsa”
A cikin hakkin Annabi Shu’aibu yayin da ‘ya’yansa mata suka nemi ya dauki Annabi Musa aiki “ya Baba, karfinka ya yi rauni, da za ka dauki wannan mutumin jarumi kuma amintacce.”
Ubangiji yake cewa Annabi (SAW), “ka yi hakuri kamar yadda ma’abota himma suka yi na daga Annabawa.” Ya kara fada “mun ba wa Annabi Ibrahim, Ishak da Yakub kuma dukkansu mun shiryar da su, mun shiryar da Annabi Nuhu kafin su, yana daga cikin zurriyarsa, Annabi Dawud da Sulaiman da Ayyuba da Yusuf da Musa da Haruna, haka muke saka wa muhsinai. Daga cikin zurriyarsa akwai Zakariya, da Yahya da Isa da Ilyas, dukka suna daga cikin Annabawa, da Ismail da Yasa’a da Yunusu da Ludu, dukkansu mun fifita su a bisa halittar zamaninsu, da Iyayen wadannan da zurriyarsu da ‘yan uwansu duk mun zabe su kuma mun shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya, wannan ita ce shiriyar Allah da yake shiryar da wanda ya so daga cikin bayinsa, wadannan Annabawan nawa, da sun yi shirka (ta ganin wanin Allah ba ta bautar guma ka ba) da duk aikinsu ma sai in zubar, wadannan su ne wadanda muka bai wa littafi da hukunci da Annabta, in mutanenka (Ya Rasulullahi sun kafirce da wannan addini, hakika mun wakilta wasu a kan addinin wadanda ba za su kafirce ba), wadannan Annabawa, su ne wadanda Allah ya shiryar, kai ma (Ya Rasulullahi) ka yi koyi da su cikin Addini – ba a Shari’a ba.” Annabi (SAW) ‘Akibu ne kuma Mukaffa ne’, meye bambancinsu? Akibu, ma’ana mai bi wa Annabawa cikin aike, daga wannan sai wannan. Mukaffa, ma’ana mai bi wa Annabawa cikin Ma’arifa, irin yadda Annabi Adamu, Nuhu,… suka yi Ma’arifa, shi ma haka ya yi.
Annabi (SAW) shi kadai, ya tattara Ma’arifar Annabawa 124,000. Allah Tabaraka wata’ala ya sifanta Annabawa da irin wadannan siffofi da muka ambata a baya masu yawa na daga gyara da shiriya da zabi da hukunci da Annabta.
Girma yakan zama na kyawun jiki, kyawun hali, Dangi tare da Hasaba (Mai kudi, Malami ko wata Sana’a da mutum yake alfahari da ita) amma duk mafi kyawun wadannan girma shi ne kyawun dabi’u. Ubangiji tabaraka wa ta’ala ya fada cikin yabon halin Annabawa da yake yi, “… sai Mala’iku suka yi wa Annabi Ibrahim Bushara da yaro Malami (Ishak), ya kara da yi masa Bushara da Yaro Mai Hakuri (Isma’ila).”
Ubangiji ya fada, “Hakika mun fitinanci mutanen Fir’auna kafin Kuraishawa wanda muka turo musu Annabi mai girma sai suka kafirce masa – sai ya zama fitina mai girma,” sakon da Annabin ya fada musu shi ne, “ya ku bayin Allah, ku ba ni zuciyoyinku, ni ma’aiki ne amintacce a wurinku.”
Ubangiji ya fada cikin hakkin Annabi Isma’ila, “…za ka same ni cikin masu hakuri” ya fadi haka ne yayin da Mahaifinshi Annabi Ibrahim (AS) ya ce masa “ya dana, na gani a mafarkina an ce in yanka ka”, ya kara fada cikin hakkin Annabi Isma’ila, “… lallai shi Isma’ila mai gaskiyar alkawari ne kuma ma’aiki ne ya kasance yana horon iyalinsa da yin Sallah da zakkah, shi yardajje ne a wurin Allah.”
A cikin hakkin Annabi Musa, Ubangiji ya fada, “shi tsarkakakke ne, kuma Annabi ne ma’aiki”. A cikin Annabi Sulaimana, Ubangiji ya fada,“madalla da bawanmu, lallai shi mai yawan komowa izuwa gare mu ne.” Ubangiji ya fada, “ka ba ni labari a cikin kur’anin nan naka, bayinmu Ibrahim da Ishak da Yakubu, suna da karfin ibada kuma suna da idon zuci (Arifai ne), mu muka tsarkake su, muka ba su tsantsar tunanin lahira, su din nan a wurinmu, wallahi suna daga cikin zababbu.”
A cikin Annabi Dawud (AS), Ubangiji ya fada, “madallah da bawanmu, shi mai yawan komawa izuwa gare mu ne.” Ya kara da cewa, “mun karfafi mulkin Dawud, mun ba shi hikima (Ma’arifa, Ilimi da yadda zai yi sana’a) da rarrabe Magana.”
Shehu Ibrahim Inyass (RTA) yana cewa, mutane biyu Allah ya fada a cikin Alkur’ani karara ya ba su Kalifanci, su ne: Adamu da Dawud, sabida rikicin kalifanci, haruffan rubuta sunansu a Larabci sai suka hargitse babu wanda ya hadu da wani (A Da Mu, Da Wu Du).
Ubangiji ya fada cikin hakkin Annabi Yusuf, “Yusuf ya ce, ya sarki dora ni a kan taskar kasarka, ni masani ne mai kiyayewa.” Malamai suka ce, babu laifi in mutum Allah ya masa baiwa da wani abu ya fada, godiya ce ga ni’imar Allah haka kuma wanda bai sani ba shi ma ya fada don kar ya hallakar da jama’a. Misali, mafarkin Sarkin Misra da aka kira masu fassarar mafarki suka ce, ‘mafarkin sanyi ne kawai’ da masani Annabi Yusuf ya zo, sai ya bayyana cewa, tattalin arzikin Misra ne na shekaru Allah yake nuna wa Sarki.