• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Ba A Fada Ba Game Da Mummunar Ambaliyar Ruwan Mokwa

byRabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
4 months ago
Mokwa
  • Ana Ci Gaba Da Tsinto Gawarwaki -NSEMA
  • Muna Tsananin Bukatar Tallafi – Al’ummar Yankin

Har yanzu ana cin karo da abubuwan ban tsoro da fargaba game da wannan ibtila’i da ya afku a Makwa wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dimbin dukiya. Daga cikin abubuwan fargaba su ne, tunanin kamuwa da cututtuka ta hanyar shakar warin gawarwakin matatun da suka makale wala’alla a cikin wani rami ko kuma a cikin ruwan da har yanzu ake a ci gaba da tsamo su.

Abubuwan ban tsoron kuma sun hada da ci gaba da samun matattu ko ganin sassan jiki a wasu wurare da ba a yi tsammani ba.

Wasu daga cikin wadanda suka afka a mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a ranar Laraba a Tiffin Maza da Angwan Hausawa na garuruwan Makwa da Rabba sun bayyana yadda suka tsira daga bala’in.

Sun kuma yi magana game da halin da suke ciki, na radadi, asara da fargaba ga LEADERSHIP Sunday.

Sun bayyana fargabar yiwuwar barkewar wata annoba yayin da warin wasu gawarwakin da ke rubewa suka cika yankunansu.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Daya daga cikin abin da ya fi tayar wa da mutanen hankali shi ne Malam Hassan Yusuf wanda ke da makarantar Islamiyya a yankin.

Ya bayyana cewa har yanzu ba a gano dalibansa guda 20 ba bayan kwana uku da ambaliyar ruwan da ta lalata dukiya ta miliyoyin Naira tare da raba dubban mazauna garin da muhallansu.

Ya ce, “Muna da makarantun Islamiyya hudu a nan, ban ga yara 20 daga cikin almajirai na ba, wasu kuma sun rasa almajirai, me zan ce wa iyayensu, wasu daga wajen Jihar Neja suke?

Alamu sun nuna cewa kimanin dalibai 40 daga cikin daliban makarantar allo da ke cikin al’ummomin ne ambaliyar ruwan ta tafi da su.

Yusuf wanda ya kasa samun natsuwa, ya ce yana nan yana addu’ar a nemo daliban.

Wata da ta tsira, mai suna Fatima Ishak, ta ce dukkan gidajen da ke unguwarsu ruwa ya tafi da su.

“Ni da ‘ya’yana biyu da mijina, duk mun tarwatse, a halin yanzu muna fuskantar wahalar rayuwa. Dukkan mu ruwa ya yi awon gaba da mu,” in ji ta.

Wani wanda abin ya shafa, Abdullahi Idris, ya shaida wa LEADERSHIP Sunday cewa: “Ko da yake ya tsira da ransa amma na rasa makwabtana, ba mu taba tsammanin wani bala’i irin wannan ba.”

A halin da ake ciki, wasu mazauna garin da aka zanta da su, sun bayyana fargabar kamuwa da cuta, saboda warin kayayyakin da ambaliyar ta shafa da har yanzu gawarwakinsu ke wasu wurare.

Wani mazaunin unguwar, Yusuf Ahmodu ya ce, “Tun da lamarin ya faru a ranar Laraba, wasu daga cikinmu da ke kewayen Angwa Hausawa da Tiffin Maza yanzu muna fargabar barkewar annoba da kuma wata ambaliyar ruwan.”

Audu Idris, ya ce, “Kuna jin warin daga nesa. Akwai dabbobi masu hadari wadanda watakila su ma ruwan ya ci sun biyo cikin wannan ambaliya.”

Mazauna garin da dama na cikin fargabar barkewar annoba sakamakon gawarwakin da suka fara rubewa da har yanzu ba a kwashe su daga gine-ginen da suka ruguje.

Bayanan da aka sabunta na adadin wadanda suka mutu da kuma wasu da aka gabatar wa tawagar gwamnatin tarayya da ta ziyarci yankin a jiya ya nuna cewa gidaje 503 ne ambaliyar ta shafa.

 

Yanzu haka yankin na fargabar barkewar annoba da kuma wata ambaliyar ruwa.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu iyali sun rasa ‘ya’yansu biyar a ambaliyar, sannan wata shahararriyar makarantar Islamiyya da ke Angwuwan Hausa ta yi asarar dalibanta 40 da ke tsakanin shekaru takwas zuwa 16.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar a cikin rahoton da LEADERSHIP ta gani a Lahadin da ta gabata ta bayyana cewa gine-gine 265 ne gaba daya suka tafi a cikin al’ummomin uku da ambaliyar ta shafa.

A halin da ake ciki, mataimakin gwamnan Jihar Neja Yakubu Garba a jiya ya karbi bakuncin tawagar gwamnatin tarayya zuwa jihar.

Mataimakin gwamnan ya shaida wa tawagar cewa kawo yanzu an tsamo gawarwakin mutane 151 daga ambaliyar, ya kuma bukaci da a sa baki wajen kara kai dauki ga al’umma da wadanda abin ya shafa.

Tawagar gwamnatin tarayya ta samu jagorancin Ministan Yada Labarai Da Wayar Da Kan Jama’a Na Kasa, Alhaji Mohammed Idris Malagi, da kuma Ministan Harkokin Jin Kai, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatdo.

Garba ya shaida wa tawagar cewa: “Rahotanni sun nuna an gano gawarwaki 151 kuma an binne su, mutane 3018 sun rasa matsugunansu, gidaje 513 ne abin ya shafa, al’ummomi uku da abin ya shafa sun hada da Tiffin Maza da Anguwan Hausawa na garin Mokwa, sai kuma Rabba inda aka samo gawarwaki 36, mutane 11 suka samu raunuka yayin da ambaliyar ruwan.”

Da yake lura da cewa har yanzu ana ci gaba da tantancewar, mataimakin gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince da buhunan shinkafa 6,000 da sauran muhimman kayayyakin da za a raba domin rage radadin bala’in.

A yayin da ya ke bayyana cewa har yanzu ba a zayyana ainihin musabbabin ambaliyar ba, ya yaba da yadda NEMA da sauran kungiyoyin da abin ya shafa suka yi gaggawar isa wurin domin ba da agaji.

 

Tinubu, Sanata Da Sauarnsu sun mika sakon jaje da ta’aziyya ga wadanda suka tsira

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a Na Kasa Mohammed Idris ya mika sakon ta’aziyyar Shugaba Tinubu ga gwamnati da al’ummar jihar.

Ministan ya ce Tinubu ya yi bakin ciki da faruwar lamarin, “Muna nan bisa umarnin mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, na cewa mu zo mu ga al’ummar jihar Neja musamman gwamna da jami’an gwamnatin jihar, domin mu jajanta muku kan abin da ya faru a Karamar Hukumar Mokwa.

“Mai girma shugaban kasa ya damu da faruwar lamarin, kuma a jiya ya ba da umarnin a kai duk wani dauke da ya dace na gwamnatin tarayya a Mokwa, shi ya sa kuke ganina tare da dan uwana, ministan harkokin jin kai,” in ji shi.

Ya kara da cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta gudanar da cikakken nazari kan lamarin tare da tattara kayan aiki domin kai dauki cikin gaggawa da tallafi ga al’ummomin da lamarin ya shafa.

“Muna sane da cewa NEMA na hada kai da gwamnatin jihar domin ganin an gudanar da ayyuka ba tare da wata matsala ba, sun tabbatar da cewa an samto gawarwakin wadanda suka rasa rayukansu cikin girmamawa, an kuma kula da wadanda suka samu raunuka daban-daban, sannan kuma ana samar da duk wani matakin da ya dace don tallafawa ‘yan uwanmu maza da mata a Mokwa,” in ji shi.

Idris ya bayyana cewa, shugaban ya nuna matukar damuwarsa kan yadda bala’in ya yi kamari, musamman ganin yadda lamarin ya faru ne kasa da shekara guda bayan wani lamari makamancin haka ya haifar da barna a wasu al’ummomi a fadin Jihar ta Neja.

Ya ce gwamnatin tarayya na aiki tukuru domin ganin an samar da isassun shirye-shirye da matakan dakile aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.

Ministan ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya umurci hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) da ta hada kai da gwamnatocin jihohi a fadin kasar domin kara wayar da kan jama’a musamman a al’ummomin da ke kusa da filayen da suke ambaliya domin tabbatar da cewa mazauna yankin sun bi alamun gargadin farko da kuma daukar matakan kariya.

“Wannan kuma kira ne ga mutanenmu da su dauki wannan a matsayin gargadi game da abubuwan da za su faru nan gaba, musamman wadanda ke zaune a yankunan da ke fuskantar irin wannan bala’i,” in ji shi.

Idris ya yaba wa gwamnatin jihar Neja da hukumominta bisa daukar matakin gaggawar da suka yi dangane da bala’in.

A nasa jawabin, Farfesa Yilwatda ya ce gwamnati na duba karin hanyoyin tallafawa ‘yan gudun hijirar.

Ya bayyana cewa an umurci hukumar kula da ‘yan gudun hijira, ta karbi ragamar hukumar NEMA wajen ci gaba da kula da wadanda bala’in ya raba da muhallansu.

A nasa martanin, mataimakin gwamnan Jihar Neja, Garba, ya gode wa shugaba Tinubu kan yadda ya gaggauta shiga tsakani a lokacin bala’in, inda ya bayyana hakan a matsayin wata manuniya ta irin jajircewar da gwamnatin ta yi wajen kyautata rayuwar ‘yan kasa a lokutan rikici.

Malam Garba ya ce al’ummar Jihar Neja sun shiga cikin mawuyacin hali sakamakon arnar da ambaliyar ruwan Mokwa ta yi.

 

Adadin wadanda suka mutu na ci gaba da karuwa

Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, NSEMA, ta sanar da samun karin gawarwaki a karkashin wata gada wadda ta kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 153 a ambaliyar ruwan.

Babban Daraktan Hukumar ta NSEMA, Abdullahi Baba Arah ne ya bayyana haka a jiya yayin da yake bayar da bayanai na yau da kullum kan Bala’in.

Ya ce, “An sake gano wasu gawarwaki biyu da yammacin a ranar (Asabar) a karkashin gada, kuma an yi jana’izarsu da safiya.

Babban daraktan ya ce, a halin yanzu, adadin wadanda suka mutu ya kai 153, kuma adadin wadanda abin ya shafa ya kai 3,018.

Ya ce a kauyen Ndayako, ba a samu rahoton mutuwar mutane ba, amma mutane 98 ne suka rasa matsugunansu, sannan kuma gidaje 58 ruwa ya yi awon gaba da su.

A Raba, ya ce gidajen da abin ya shafa 5 ne, amma gadar da ke zuwa yankin ruwa ya tafi da ita.

Shugaban ya kuma ce za a ci gaba da aikin neman agaji da ceto, yayin da aka aiwatar da bayar da abin da aka samu na wucin gadi ga wadanda ambaliyar ta shafa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Saƙon Barka Da Sallah: Tinubu Ya Baiyana Tabbacin Ci Gaban Nijeriya, Da Sauyin Tattalin Arziƙi

Saƙon Barka Da Sallah: Tinubu Ya Baiyana Tabbacin Ci Gaban Nijeriya, Da Sauyin Tattalin Arziƙi

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version