• English
  • Business News
Monday, May 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abubuwan Da Za Su Iya Kawo Cikas Ga Bukukuwan karamar Sallah

by Idris Aliyu Daudawa
1 month ago
in Labarai
0
Abubuwan Da Za Su Iya Kawo Cikas Ga Bukukuwan karamar Sallah
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sallah bikin daya rana Sallah mai yawan baya,ta wuce ta bar Wawa da bashi haka lamarin yake amma sai idan ba a sa hakuri a gaba ba ne,sai an samu haduwa da matsala,sanin kowa ne da zarar an dawo daga masallacin Idi,to Sallah ta kare ke nan,amma wannan ga shi maigida,sauran kuma sai a bar wa kananan yara dama sune za su rika zuwa yin yawon Sallah.

Ko shakka babu kamar yadda masu iya magana suka ce ta wuce ta bar Wawa da bashi,domin shi ne zai ce bani kaza,bani bashi sai bayan Sallah.Bayan Sallar ai ba wuya ke gare shi ba,a ranar ce fa wanda ya amshi bashin zai fara wasan ‘yar vuya shi da wadanda ya amshi bashin daga wurinsu.

  • Sallah: ’Yansanda Sun Yi Alƙawarin Tabbatar Da Tsaro A Kano
  • Yobe Ta Bayyana Ɗaukar Matakan Tsaro A Lokacin Bikin Sallah

Yayin da aski ya riga ya kai ga zuwa gaban goshi ya fi zafi, hakanan ma al’umma musamman Magidanta sun fara shirye- shiryen yadda za su gabatar da Sallar tavangaren kayan sawa ranar Sallar wato sutura,sayen kayan abinci wadanda a halin da ake ciki yanzu lamarin ya zama wani abu da ake kira”Sai mai da ka sha”domin ita Rijiya ce saboda tsananin nisanta idan ba danka wanda ka haifa ba,babu wanda zai iya zuwa can ya debo maka ruwa ka sha.

Wadannan abubuwan za su iya kawo cikas ga bukukuwan karamar Sallah mai zuwa sun kuma  hada da 1.Rashin kudade, 2 tsadar rayuwa,3 matsalar tsaro 4.Al’umma da dama basa garuruwan su na asali.

Rashin kudade a hannun jama’a babbn abinda yafi damuwar mutane a wannan halin da muke ciki shi ne rashin kudade,domin kuwa kafi a cire tallafin man fetur,a watan Mayu na 2023 cikin jawabin da yayi bayan rantsar da sabon Shugabn kasa Bola Ahmed Tinubu, kashegari kuma sai al’amuran rayuwa suka fara sauyawa musamman ma farashin kayan da suka yi tashin gwauro Zabo,har ya zuwa yanzu kuma abubuwan  kara tashi sama suke yi maimakon su dawo kasa-kasa.Kafin dai,a cire tallafin mai din mutane da yawa suna da sana’oinsu na kanana da matsakaita sai dai kuma sannu a hankali wanda/wadanda suke tafiyarda rayuwarsu tare da ta wasu suka kasa tafiyar da tasun ma,wadanda suke daukar dawainiyar wasu ba tasu ba kadai su suka koma suma wasu suka sawa rai su samu daga gare su.Duk karin kudin mai bayan cire tallafi sai wasu mutane masu kananan sana’oi suka rasa yadda zasu ci gaba da yin sana’ion sai abubuwansu suka tsaya cak babu gaba bare ayi maganar wata baya. Hakanne zai sa a wannan sallah wasu sai dai su gani ana yi a gidajen wasu saboda kuwa abinda za su sa ma bakinsu ya gagare su.

Labarai Masu Nasaba

Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi

2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido 

Tsadar rayuwa tun daga wancan lokacin ne bayan cire tallafin mai,da kwana daya kawai zuwa biyu sai rayuwar wasu dole ta fara sauyawa,kaya ko kayayyakin da ake saya a farashi na kashi 75 zuwa 100 sai abin ya koma farashin wasu har sai da,ya kai kashi 200 zuwa kashi 300 kai wani abin ma, har ya zarce haka,kuma kamar yadda Hausawa suka ce dole ce kanwar na ki ta sa hakan ta kasance,wannan kuma haka ne. Dole ce tasa haka saboda har an kai ga ganin abinda ya cirewa Buzu nadi wato wahala ke nan.Kuma dole ne cin kasuwa da makiyi wasu abubuwan abin ba,a  iya cewa komai sai dai ayi gum da Baki kawai.

Matsalar tsaro

Ko shakka babu lamarin tavarvarewar tsaro ba karamin koma baya ya kawo ba na lamarin zamantakewa tsakanin al’umma abu tun daga wannan unguwa zuwa waccan har,ta kai ga daga wannan babban gari ma zuwa wancan har ta kai ga daga wannan Jiha zuwa waccan.Irin halin da al’umma suka tsinci kansu ke nan lamarin da ya kan yi tafiyar Kura yadda take gaba sai ta koma baya. Arewa ta sassa daban- daban tana fama da matsalar data shafi tsaro  tunda kuwa ana yin garkuwa lokaci,anan matafiya wasu Jihohi na sashen Arewa maso yamma kamar Kaduna, Katsina,Zamfara,Sakkwato,da kuma Kebbi,masu ta shi daga Abuja zuwa gida wasu suna kan hanyar tasu ake tsaida su a kwashi mutane kamar Dabbobi ayi cikin daji dasu,kai har ma,ta kai ga mutane ko,a gidajensu suke basu tsira ba ana iya zuwa kowane lokaci ayi awon gaba dasu sai kuma yadda Allah yayi.Yayin  da wasu suna dawowa wasu kuwa sun tafi ke nen sai dai  aji labarin an kashe su,wasu ko ma an kai kudin fansar ba,za’a sake su ba.Irin hakan ce ta sa wasu yanzu basu zuwa gida Sallah saboda tsoron aukuwar irin hakan,maimakon hakan sai su yi hakuri su rungumi kaddara ta yin rayuwa kamar irin cikin halin,da suka samu kansu.

Tafiya zuwa yawon Sallah daga wannan unguwa zuwa waccan ko daga wannan gari zuwa wancan,halin da ake ciki yanzu hakan bata yiyuwa ba domin komai ba sai saboda tsoron irin abinda ka iya faruwa gare su,maganar gaskiya yanzu lamarin tsaro ya sa mutane da yawa sun,shiga cikin halin tsoro saboda komai yana iya faruwa a lokacin da ba ayi tsammanin hakan ba.Ba ance babu tsaron bane gaba daya amma su wadannan masu tayar,da zaune tsaye ko ina suna iya zuwa saboda ai suna da wadanda suke basu halin da ake ciki da su kan samu na su kason idan an yi sa’ar dauka da kuma garkuwa da mutane aka kuma biya kudin fansar.

Al’umma da dama basa garuruwan su na asali

Mutane da dama yanzu wasu ma ba Jihar su ta asali suke ba,wasu suna wata Jiha,kai akwai ‘yan Nijeriyar da har yanzu suna kasashen Nijar ko kuma Kamaru,idan ma sun yi sa’ar suna Jihar tasu ne,to su kan kasance ne a wani sansanin ‘yan gudun hijira ne wato wuraren da aka tsugunnar dasu,sanin kowa ne,babu yadda rayuwa za ta yi daidai ga wasu a,irin wadancan wuraren saboda can ma din da akwai nau’oin matsalolin da suke fuskanta a can.Ana iya tunawa shifa sansanin ‘yan gudun hijira wuri ne da aka ware na musamman wanda ake taimakawa nau’oin mutanen da suka fuskanci matsala babu yadda za su iya yi wajen tafiyar da rayuwarsu.Daga karshe sanin kowa ne duk wanda bai garin shi na asali rayuwa Lami yake yin ta domin a matukar takure yake.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AzumiSallah
ShareTweetSendShare
Previous Post

Shugaban CMG Ya Gana Da Ministar Raya Al’adu Ta Rasha

Next Post

An Fitar Da “Takardar Ci Gaban Sha’anin Hakkin Dan Adam A Xizang A Sabon Zamani”

Related

Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi
Labarai

Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi

15 minutes ago
Ganduje Ya Zargi Gwamna Yusuf Da Ɗaukar Nauyin Zanga-zanga A Kano
Manyan Labarai

2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido 

1 hour ago
Zamfara Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Kula Da Aikin 2025 Domin Kyautata Jin Dadin Alhazan Jihar 
Manyan Labarai

Zamfara Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Kula Da Aikin 2025 Domin Kyautata Jin Dadin Alhazan Jihar 

3 hours ago
Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato
Tsaro

Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato

14 hours ago
Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato
Labarai

Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

15 hours ago
2027: Har Yanzu Ba Mu Saka Ranar Fara Sabunta Katin Zabe Ba — INEC
Labarai

INEC Na Samun Matsin Lamba Don Kar Ta Yi Wa TNN Rajista — Kakakinta

17 hours ago
Next Post
An Fitar Da “Takardar Ci Gaban Sha’anin Hakkin Dan Adam A Xizang A Sabon Zamani”

An Fitar Da “Takardar Ci Gaban Sha’anin Hakkin Dan Adam A Xizang A Sabon Zamani”

LABARAI MASU NASABA

Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi

Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi

May 12, 2025
Ganduje Ya Zargi Gwamna Yusuf Da Ɗaukar Nauyin Zanga-zanga A Kano

2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido 

May 12, 2025
Zamfara Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Kula Da Aikin 2025 Domin Kyautata Jin Dadin Alhazan Jihar 

Zamfara Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Kula Da Aikin 2025 Domin Kyautata Jin Dadin Alhazan Jihar 

May 12, 2025
A Koyi Darasi Daga Tarihi

A Koyi Darasi Daga Tarihi

May 11, 2025
Kada A Bata Ran Mahaifiya

Kada A Bata Ran Mahaifiya

May 11, 2025
Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato

Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato

May 11, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka

May 11, 2025
Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

May 11, 2025
Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

May 11, 2025
Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4

Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4

May 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.