Wasu alkaluma da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta fitar, sun nuna yadda adadin kamfanonin fasahar AI da aka yiwa rajista a kasar Sin suka kai sama da 5000, adadin da ya karu matuka kan sama da 1,400 da kasar ke da su a shekaru biyar da suka gabata.
An fitar da alkaluman ne yayin taron kasa da kasa na baje kolin hajoji masu nasaba da na’urori masu basira, wanda ke gudana yanzu haka a birnin Chongqing na kudu maso yammacin kasar Sin.
Da yake tabbatar da hakan, mataimakin ministan ma’aikatar Xin Guobin, ya ce an kafa masana’antu masu aiki da na’urori masu basira sama da 40,000 a kasar Sin, da yankunan gwaji na kirkire-kirkiren AI da aiki da su 11, da kuma yankunan gwaji a matakin kasa na ababen hawa masu aiki da fasahohin AI har 17.
Xin, ya kara da cewa gwamnatin Sin ta kaddamar da asusun jarin bunkasa masana’antun AI mai kunshe da kudin Sin yuan biliyan 60, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 8.4, tare da kiyaye manyan dokokin cin gajiyar fasahar AI, da cibiyar Sin da kungiyar BRICS ta bunkasa fasahar AI da inganta hadin gwiwa, da ma sauran manyan sassan fasahohin AI sama da 240. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp