Kakakin hukumar lafiya ta kasar Sin Mi Feng, ya ce adadin mutanen dake kamuwa da cuttuttukan numfashi masu neman jinya a cibiyoyin lafiya a fadin kasar na raguwa a cikin ‘yan kwanakin nan. Jami’in ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai na hukumar a yau Lahadi ranar 24 ga wata.
Bayanai sun nuna cewa, a ranar 22 ga watan Disamba, jimillar adadin marasa lafiya masu fama da cututtukan numfashi dake neman jinya a cibiyoyin lafiya dake gundumomi, da birane a fadin kasar ya ragu da kashi 8.2%, idan aka kwatanta da na daidai wannan lokacin a makon da ya gabata, kana ya ragu da kashi 30.02% bisa na lokacin kololuwar fama da matsalar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp