Kamfanin jiragen kasa na kasar Sin, ya ce cikin watanni 11 na farkon shekarar bana, adadin zirga zirgar fasinjoji ta jiragen kasa a kasar ya haura biliyan 4, alkaluman da suka kai kololuwa a tarihi.
Kamfanin ya ce yayin da ake kara fadada zamanantar da layukan dogo a kasar, adadin tsayin layukan dogo da jiragen kasa ke bi a kasar ya haura kilomita 160,000, ciki har da na jirage masu matukar gudu da ya kai kilomita 46,000.
Kasar Sin ta gina, tare da fara amfani da sama da tashoshin layin dogo 3,300 a sassan kasar daban daban, ciki har da na jiragen kasa masu matukar gudu sama da 1,300. (Mai fassara: Saminu Alhassan)