Hukumar lura da sufurin jiragen kasa ta kasar Sin, ta yi hasashen samun adadin zirga-zirgar fasinjoji ta jiragen kasa sama miliyan 80.5, yayin kwanaki biyar na hutun bikin Duanwu ko bikin tseren kwale kwale na bana.
An fara samun dandazon matafiya ta jiragen kasa a kasar Sin tun daga yau Juma’a, kwana guda gabanin kwanakin hutun uku, yayin da ake sa ran kaiwa kololuwar yawan matafiyan a gobe Asabar, inda ake hasashen adadin zirga-zirgar zai kai kusan miliyan 18.3.
Alkaluma daga kamfanin 12306, mai samar da hidimar yankar tikitin jiragen kasa na kasar Sin, sun nuna wuraren da matafiya suka fi yankar tikitin zuwa, wadanda suka hada da biranen Beijing, da Shanghai, da Guangzhou, da Chengdu, da Hangzhou. Sauran su ne Wuhan, da Xi’an, da Nanjing, da Changsha da kuma Zhengzhou. (Mai fassara: Saminu Alhassan)