A ranar Litinin ne shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya ki cewa Uffan kan dalilin da ya sa jam’iyyar ta mika sunan shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan da Godwill Akpabio ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.
An mika sunan Lawan da Akpabio ga INEC duk da adawar da ake yi na cewa ba su shiga zaben fidda gwani na sanata na APC ba.
Amma da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a Villa bayan gabatar da zababben gwamnan jihar Ekiti ga shugaban kasa Muhammadu Buhari. Adamu ya ki cewa uffan kan dalilin Jam’iyyar na sauya sunayen wadanda ake zargin sun lashe zaben fidda gwanin.
Da aka tambaye shi tayaya Lawan ya fafafa a takarar Sanata, Adamu ya ce: “Kada ka kai kanka gaban kotu. Waya fada hakan, ko ka ji wasu suna cewa hakan ne?
“Shin akwai wata doka da ta ce idan ka tsaya takara ka fadi ba zaka sake tsayawa wata takara ba?”
“Ku je ku nemo wanda ke da alhakin shirya zaben Fidda Gwanin. Ni na yi iya hurumi na.