Dan wasa Cristiano Ronaldo ya fara sabuwar rayuwar sa ta kwallon kafa a kasar Saudiyya bayan da a ranar Talatar data gabata ya samu karba mai kyau daga magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr dake buga babbar gasar kasar Saudiyya.
Ronaldo, mai shekara 37 a duniya ya sauka a kasar Saudiyya ne tare da farkar sa, wato Georgina Rodriguez, ‘yar asalin kasar Spain kuma za su shafe Shekaru biyu da rabi a kasar inda zai karbi albashin kusan dalar Amurka miliyan 200.
Sai dai zaman Ronaldo da farkar tasa Georgina Rodriguez a Saudiyya yana tattare da tambayoyi.
Wacce Doka Zasu Karya?
Ronaldo dai da Georgina Rodriguez ba suyi aure ba har yanzu duk da cewa sun haifi ‘ya’ya saboda haka zaman su a Saudiyya a daki daya kamar karya doka ne amma a Saudiyya.
A Saudiyya, haramun ne rayuwa a daki daya tsakanin na miji da mace idan har babu aure a tsakanin su.
Sai dai kamar yadda rahotanni suka tabbatar wasu manyan lauyoyi guda biyu sun nuna cewa shugabanni a kasar zasu iya kawar da kansu akan wannan.
Me lauyoyi suka ce?
“Shugabannin yanzu basa tsoma baki a irin wannan maganar musamman akan wadanda ba ‘yan kasa ba, sai dai duk da haka doka ta hana mace da na miji rayuwa a daki daya” in ji wani kwararren lauya
Shin Ronaldo zai auri Georgina Rodriguez?
Ronaldo ya taba bayyana cewa yana da burin auren Georgina Rodriguez, duk da cewa bai bayyana lokacin da ya shirya yin auren ba.
A wata hira da Ronaldo yayi da Piers Morgan a watan Nuwamban shekarar data gabata, Ronaldo yace baya tunanin yin aure yanzu amma yana ganin nan gaba zai aure ta saboda yana ganin kamar ya cancanta ya aure ta itama ta cancanta ta aure shi
“Amma abune wanda baya tsari na a yanzu amma a nan gaba zanyi” inji Ronaldo.