Mai Martaba Etsu Nupe, Dakta Yahaya Abubakar ya bukaci al’ummar Nijeriya su dage da addu’a, musamman a wannan lokaci da ake ganin yadda rashin tsaro ya yi kamari a kasar nan.
Etsu Nupe ya ce babu wani abin da ya dace da jama’a a daidai wannan lokaci face addu’a ganin yadda rashin zaman lafiya da satar mutane don karbar kudin kansa da sauran fitintunu suka yi katutu a sassa daban-daban da ke kasar nan.
Sarkin ya yi wadannan kalamai ne a wani shiri da gidan Talabijin na Liberty Kaduna ya yi da shi wanda wakilinmu ya kalato mana.
Ya kara da cewa zaman lafiyar kasar nan shi ne abin da zai kawo ci gaban ta, kama daga mutunta addinan juna da kaucewa abin da zai kawo rabuwar kai.
Da yake magana a kan zaben 2023 kuwa, mai martaba ya bayyana cewa yin katin zabe shi ne a matsayin makamin da al’umma za su yi amfani da shi domin zabar shugabanni nagari wadanda za su ciyar da kasar nan gaba.
Daga karshe ya kara jaddada bukatar da ke akwai wajen gwamnati ta kara himma don kawo karshen matsalar tsaro a kasar baki daya.