Themba Zwane ne ya zura kwallaye biyu a cikin mintuna 16 na farkon rabin lokaci yayin da Afrika ta Kudu ta lallasa kasar Namibiya da ci 4-0 inda ta samu maki uku rigis a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023 (AFCON).
Tun a minti na 10 da fara wasan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Al Ahly ta kasar Masar Percy Tau ya jefa kwallo a wani bugun daga kai dai mai tsaron raga.
Thapelo Maseko wanda ya shigo daga baya ya jefa ta hudu a lokacin da mai tsaron ragar kasar Namibiya Lloyd Kazapua ya ture wata kwallo da aka buga masa.
Talla