Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta buga canjaras a wasanta na farko a gasar AFCON ta bana inda ta buga da kasar Equatorial Guinea a filin wasa na Olympic Alassane Outara da ke birnin Abidjan.
Dan wasan Equatorial Guinea Ivan Salbado ne ya fara jefa kwallo a ragar Nijeriya a minti na 36 da fara wasan.
- Yadda Aikin Gine-gine Na Kasar Sin Suka Taimaka Wajen Gudanar Da Gasar Cin Kofin Afirka
- AFCON 2023: Ma Su Masaukin Baki Sun Doke Guinea Bissau Da Ci 2-0
Amma minti biyu tsakani Victor Osimhen ya farke wa Nijeriya kwallonta inda ya jefa kwallon da Ademola Lookman ya bashi a ragar abokan karawar.
Hakan yasa Nijeriya ta koma matsayi na uku a rukunin A na gasar AFCON.