Tawagar Super Eagles ta Nijeriya zata hadu da Elephants ta kasar Cote de’Voire a wasan karshe na gasar kofin kasashen Afirika da za a buga a ranar Lahadi 11 ga wata Fabrairu.
Super Eagles sun kai wannan matsayi ne bayan da suka doke kasar Afirika ta Kudu a bugun daga kai sai mai tsaron raga a ranar Laraba yayin da ita kuma Cote de’Voire ta doke kasar Congo da ci daya mai ban haushi.
Kasashen biyu sun hadu da juna a wasannin rukuni da aka buga kuma zasu sake haduwa domin tantance wanda zai lashe kofin kasashen Afirika na bana, a filin wasa na Alasane Outara da ke birnin Abidjan a ranar Lahadi.