Wani jami’in cibiyar rigakafi da yaki da annobar cututtuka ta Afirka, watau Africa CDC ya yaba da kasar Sin a matsayin babbar abokiyar huldar cibiyar kula da lafiya ta yankin.
A gefen taron shekara-shekara na cibiyar kula da lafiyar jama’a ta yankin kudancin Afirka, watau NPHI da aka gudanar a birnin Harare na kasar Zimbabwe, darektan cibiyar CDC ta Afirka Lul Riek, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasar Sin ta ba da tallafi sosai wajen gina ababen more rayuwa ta kiwon lafiya.
- Wannan Imanin Ne Ya Kai Likitocin Sin Nahiyar Afirka…
- An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” A Italiya
Riek ya ce, “Kasar Sin babbar abokiyar hadin gwiwa ce ga aikin cibiyar CDC ta Afirka. An yi nasarar gudanar da kyawawan ayyukanmu na gaggawa da kuma samar da cibiyar yaki da annabor cututtuka a kasar Habasha ne saboda hadin gwiwar da muka yi da kasar Sin.”
An kaddamar da hedkwatar CDC ta Afirka, wacce aka amince da ita a matsayin wani muhimmin aiki na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannin kiwon lafiyar jama’a a hukumance a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, a shekarar 2023.
Riek ya yi kiran kara hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen tallafa wa kasashen Afirka da ababen more rayuwa ta kiwon lafiyar jama’a, da horarwa a kan kwazon aiki na dakunan gwaje-gwaje da gina cibiyoyin kula da lafiya na yankin kudancin Afirka. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp