Bayan cece-kuce da ta ɓarke bayan afuwar da shugaban kasa ya yi wa Maryam Sanda, wacce aka yanke mata hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a shekarar 2020 saboda kashe mijinta, Bilyaminu Bello, shugaba Bola Tinubu ya soke afuwar amma ya mayar da hukuncin kisan zuwa ɗaurin shekaru 12.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sabuwar takarda da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.
A cewar sanarwar, Sanda, wacce ta riga ta shafe shekaru shida da watanni takwas a Cibiyar Tsaron ta gyaran hali da ke Suleja a jihar Neja, an mata afuwa ne bisa dalilan tausayi. Saboda haka, yanzu za ta ci gaba da zama shekaru 5 da watanni 4 a gidan yari kafin a sake ta.
Don haka, an mayar da hukuncin kisa na Maryam Sanda zuwa shekaru 12 a gidan yari, wanda hakan ya nuna tana da kasa da shekaru shida na zama a gidan gyaran halin.














