Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabon kwamitin gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars bayan da wa’adin waɗanda ke kai ya ƙare.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau Lahadi.
- Katsina United Ta Kammala Ɗaukar Ƴan Wasa Biyu Daga Kano Pillars
- Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Naɗa Sabon Kwamitin Gudanarwa Na Ƙungiyar Kano Pillars FC
An zaɓo sabbin mambobin kwamitin gudanarwar ne duba da kwarewa tare da gogewarsu a wannan fanni na harkar ƙwallon ƙafa, inda za su yi aiki na wucin gadi na shekara guda, tare da yiwuwar sabunta kwantiragin su idan suka taɓuka abin a zo a gani.
Fitattun sunaye a cikin sabon kwamitin sune manyan masu sharhi a harkar kwallon ƙafa da harshen Hausa da suka haɗa da Abubakar Isah Dandago (Yamalash) a matsayin babban darakta a ɓangaren sadarwa ta zamani da kuma Ismail Abba Tangalashi a matsayin mataimaki.
Sai kuma kyaftin ɗin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya (Super Eagles) Ahmed Musa wanda ya samu matsayin babban jakadan ƙungiyar ta Kano Pillars inda ya taka leda a shekarun da suka gabata a ƙungiyar.
Gwamnan ya bayyana ƙwarin gwuiwar cewa waɗannan mutane za su yi amfani da ɗimbin ilimi da gogewar da suke da ita wajen tafiyar da harkokin ƙwallon ƙafa.
Ana sa ran sabon kwamitin zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ma’aikatar matasa da wasanni ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wasanni domin bunƙasa ƙungiyar ta Kano Pillars.