A yau Talata 23 ga watan Satumban nan, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gudanar da wani taron manema labarai, inda aka bayyana yadda kasar Sin ta samu ci gaba mai inganci a fannin ba da ilmi sakamakon aiwatar da shirin raya kasa na 14 na shekaru biyar-biyar. Yayin taron, ministan ilmi Mr. Huai Jinpeng ya bayyana cewa, aikin ba da ilimi na tushe na kasar Sin ya kai matsakaicin matsayi na kasashe masu arziki a duniya.
A fannin ilmin dijital kuwa, an gina babbar dandalin ilimi mai hikima wanda ya shafi kasashe da yankuna sama da 200, kuma shi ne mafi girma da inganci a duniya. Haka nan, an kulla alakar hadin gwiwar ilimi da kasashe da yankuna 183, kuma an gina “Cibiyoyin koyar da sana’o’i na Lu Ban” 36 tare da kasashen Asiya, da Afirka da Turai. Wadannan cibiyoyin sun zama sabuwar alamar Sin a duniya a bangaren ba da ilmi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp