Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kammala zagaye na goma na shirinta na musamman na aikin jinya kyauta, inda aka kula da marasa lafiya 3,447 daga sassa daban-daban na jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar 21 ga Oktoban 2025, ya ce shirin wanda aka fara shi tun watan Yuli na bara, yana bayar da jinyar kyauta ga marasa lafiya da ke fama da cuta irin su ciwon ido (cataract), kumburin mafitsara ko gambon ciki (hernia da hydrocele), da kula da masu yoyon fitsari na ‘vesico-vaginal fistula’ (VVF) tare da faxakar da jama’a kan kiwon lafiya.
- Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia
- Majalisa Ta Tabbatar Da Yusuf A Matsayin Sabon Shugaban NPC, Wasu 2 A Matsayin Kwamishinoni
An gudanar da zagayen jinya na goma a asibitoci kamar Asibitin Ƙwararru na Yariman Bakura, Babban Asibitin Gusau, Asibitin Ido na Gusau da Asibitin Farida.
Sanarwar ta ce, “Domin rage wahalhalun da al’umma ke fuskanta wajen samun kula da lafiya, gwamnatin Dauda Lawal ta ƙaddamar da wannan shiri na musamman domin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi da ke buƙatar jinya.”
Shirin, wanda aka fara a watan Agusta 2023, ya riga ya isa ga marasa lafiya sama da 3,400 zuwa asibitoci daban-daban ta hanyar tsarin ‘tele-screening’, wanda ke bai wa ƙwararrun likitoci damar lura da marasa lafiya daga ƙauyuka da yankunan karkara cikin gundumomi 14 na jihar.
Bangarorin da aka kula da lafiya a zagaye na goman da suka haɗa da; mutum 1,659 marasa lafiya masu kumburin ciki da irin sa. Mutum 1,081 masu ciwon ido da aka yi wa tiyata. Mutum 118 marasa lafiya masu cutar VVF da aka yi wa tiyata.
Sanarwar ta bayyana cewa, wannan shiri ya zama wata nasara ga gwamnatin jihar wajen kai ingantacciyar kulawar lafiya ga jama’a, musamman a yankunan da ke da ƙarancin cibiyoyin jinya.