Katafaren aikin karkata akalar ruwa daga kudu zuwa arewacin kasar Sin, wanda wani kamfanin gwamnatin kasar ya aiwatar, ya amfani sama da mutane miliyan 176.
A cewar kamfanin, hanyoyin gabashi da tsakiya, na karkatar akalar ruwan daga kudu zuwa arewacin kasar ta Sin, sun haifar da alherai masu tarin yawa, tun bayan da aikin ya karkatar da yawan ruwan da ya kai sama da kyubik mita biliyan 70 na ruwa zuwa arewacin kasar mai fuskantar barazanar fari, ta hanyoyin gabashi da tsakiyar kasar.
Kamfanin da ya kammala aikin ya kara da cewa, birane kamar Beijing da Tianjin, sun dogara kan ruwan da aikin ya samar a matsayin hanyar samun ruwa, kana aikin ya kyautata yanayin tattalin arziki da bunkasar zamantakewar manya da matsakaitan birane sama da 40. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp