Ranar 8 ga wata, shugaban kasar Philippines Ferdinand Romualdez Marcos ya sa hannu kan abubuwa 2 masu nasaba da yankin teku wadanda ake kira dokoki, sun kuma tanadi tsibirin Huangyan da yawancin tsibirin Nansha Qundao da ruwan da ke makwataka da shi cikin yankin tekun Philippines. Matakin da Philippines ta dauka, matakin ne na neman aiwatar da hukuncin da aka yanke ba bisa doka ba dangane da tekun kudancin kasar Sin ta hanyar kafa dokar cikin gida, kana mataki ne na siyasa da gwamnatin Philippines ta dauka bisa sabbin manyan tsare-tsaren tsaron kasa da manufofin diplomasiyya.
Amma Philippines ba za ta cimma burinta ba. Saboda wadannan daftarin dokokin 2 sun saba wa ikon mulkin kan kasar Sin da hakkinta na teku a tekun kudancin kasar Sin, da saba wa muhimmiyar ka’idar “daidaita sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa” da aka jaddada cikin sanarwar bangarori masu nasaba da tekun kudancin kasar Sin, da kawo tarnaki ga tsarin dokokin kasa da kasa na yanzu. Matakin Philippines, mataki ne da aka dauka ba bisa doka ba, kuma ba zai yi aiki ba.
Da ma an samu zaman lafiya, da sada zumunta da yin hadin gwiwa a tekun kudancin kasar Sin. Amma abun da Philippines ta yi ya saba wa burin al’ummomin da ke yankin. Philippines tana kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Ya zama tilas Philippines ta dakatar da abin da ta yi ba bisa doka ba, ta dakatar da duk wani matakin gashin kai na fadada takaddamar tekun kudancin kasar Sin, da sanya yankin cikin halin sarkakiya. Idan Philippines ta ci gaba da rura wuta a tekun kudancin kasar Sin, kasar Sin za ta mayar da martani. (Tasallah Yuan)