Dalibin makarantar Jami’a ta gwamnatin tarayya da ke Dutse, Aminullah Adamu wanda uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta tsare bisa zarginsa da batanci a gareta, ya nemi afuwarta bayan ta ya fe masa ta sallame shi ya koma cikin danginsa.
Aminullah an zarge shi da batancin ne a kafar sada zumunta ta Twitter yayin da yayi wani sharhi kan hoton uwargidan shugaban da cewa “… tayi bulbul” wanda hakan ya fusata uwargidan tasa jami’an tsaron sirri ta cikin gida suka yi masa sammaci.
Sai dai, a ranar Juma’ar da ta gabata, 2 ga watan Disambar 2022, Aisha Buhari ta janye karar da take yiwa Aminullah. Inda tuni aka hada shi da danginsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp