Kungiyar dattawan arewa (NEF) ta bayyana cewa akwai babban jan aiki a gaban zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Mai Magana da yawun kungiyar NEF, Hakeem Baba-Ahmed ya ce Tinubu yana da jan aikin mai matukar wahala gaske.
- Dan Majalisar Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Fita Yakin Neman Zabe A Bauchi
- Xi Ya Ba Da Sabon Tunani Da Shawarar Wayewar Kai Ta Duniya Don Inganta Zamanantar Da Daukacin Bil-Adama
Tinubu wanda shi ne dan takarar jam’iyyar APC, ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa da aka kammala, wanda ya samu kuri’u mafi yawa.
Bayan samun wannan nasara, za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu.
Sai dai kuma Baba-Ahmed ya ce Tinubu na fuskantar kalubale a fannin samun amincewar ‘yan Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali.
Da yake rubutawa a shafinsa na mako-mako, Baba-Ahmed ya rubuta cewa: “Shugaban da za a rantsar a ranar 29 ga Mayu zai fuskanci aiki mafi wahala a duniya.
“Babban kalubalensa shi ne, samun amincewa. Babu wani shugaba a ko’ina da zai iya cimma wani abu mai kima sai dai idan ya samu isassun ‘yan kasa da za su yarda cewa yana da kima kuma yana girmama su.
“Ya kamata shugaba mai zuwa ya gina nasa ginshikin gwamnatisa mai nagarta, domin Buhari ya gaza yin haka.”