• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai ‘Yancin Tofa Albarkacin Baki A Gwamnatin Tinubu – Minista

by Sulaiman
2 years ago
Minista

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta shigo da dokokin hana ‘yan jarida da sauran jama’ar Nijeriya fadin albarkacin bakin su ba.

Sai dai kuma ya ce, ya kamata mutane su sani cewa, “‘yancin faɗin albarkacin baki ya na tattare da haƙƙin sanin ya-kamata da ya rataya a wuyan kowa.”

  • Za A Kammala Aikin Bututun Iskar Gas Na AKK A Disambar 2024 – NNPC
  • Shari’un Zabe: A Kauce Wa Tarzoma Duk Yadda Ta Kaya

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya fito a karon farko aka tattauna da shi a shirin “Newsnight” na gidan talabijin na ARISE a Abuja a daren Asabar, inda ya amsa tambayoyi dangane da ƙudirorin wannan gwamnatin kan harkar yaɗa labarai da shirin wayar da kan al’umma da kuma burukan ‘yan Nijeriya.

Idris ya bayyana cewa, ya shafe makwanni takwas da su ka gabata yana nazari kan ayyukan ita kan ta Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta Tarayya, tare da tattaunawa da Sassa da Hukumomin ma’aikatar daban-daban.

Ya ce: “Mun san abin da mu ke so ta zama, amma tilas ne mu fara da fahimtar inda ta ke a yanzu, da kuma dalilin da ya sa ba ta kai inda mu ke buƙata ta kai ba.”

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

A kan batun aikin wayar da kan jama’a, ya ce, aiki ne da ke cikin alhakin da aka ɗora masa a matsayin sa na minista.

Ya ce, “Mutane su na rage yarda da gwamnati, don haka ya kamata mu tambayi kan mu, ina ne ba mu yi daidai ba? Me ya sa ‘yan Nijeriya ba su amince da Nijeriyar ba? Za mu fito da wani tsari na yadda za mu sake fahimtar ko mu su wanene kuma mu fara komawa mu amince da Nijeriya.

Da ya ke magana kan irin ƙasar da ‘yan Nijeriya su ke so su samu, sai ya ce, “Domin amsa wannan tambaya, mu na buƙatar tattaunawa a duk faɗin ƙasar nan kan irin ƙasar da mu ke muradin mu ga mun samu. Me ya sa yanzu a makarantu aka daina wajabta karanta Haƙƙin Ɗan Ƙasa, wato ‘Civics’? Wanene ɗan asalin Nijeriya? Shin mun san haka? Akwai buƙatar mu dawo da sanin kyawawan ɗabi’u da aka san mu da su.

Bugu da ƙari, ya yi tsokaci kan irin ‘yancin da jama’ar Nijeriya su ke da shi, ya ce, “Kafafen yaɗa labarai na Nijeriya su na da ‘yanci, kuma shi Shugaba Tinubu so ya ke ma ya ƙara musu ‘yanci. Yaɗa labarai ya na da muhimmanci wajen samun nasarar kowace gwamnati. Mai girma Shugaban Ƙasa ya na ƙoƙarin faɗin magana a yadda ta ke ba tare da wata ƙumbiya-ƙumbiya ba.

“Batun yaɗa labaran ƙirƙira da na ƙarya ba matsala ba ce ga Nijeriya ita kaɗai, matsala ce da ta shafi duniya baki ɗaya. Mun ga yadda yaɗa labaran ƙarya ya jawo a Amurka, wanda ya jawo harin ranar 6 ga Janairu da aka kai ainihin cibiyar dimokiraɗiyyar Amurka. Tilas ne mu tunkari matsalar yaɗa labaran ƙarya a duk duniya.

“Bari in ƙara maimaita cewa: Gwamnatin mu ba za ta ƙaƙaba wa kafafen yaɗa labarai ko sauran ‘yan Nijeriya takunkumi ba, ko ta yi wa ‘yancin ‘yan jarida zagon ƙasa. Sai dai kuma ya kamata a sani cewa, kowane ‘yanci ya na tattare ne da buƙatar mutum ya san alhakin da ke kan sa. ‘Yancin tofa albarkacin baki ya na tattare da sanin ya kamata.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati
Labarai

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba
Labarai

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Next Post
Shenzhou-16

’Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-16 Za Su Dawo Duniya Bayan Gama Mika Aikinsu 

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.