Hukumar Kula da Yanayin sararin samaniya ta Nijeriya (NiMet) da Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) sun ce akwai yiyuwar samun karin ambaliyar ruwa a wasu jihohi a cikin kwanaki masu zuwa, musamman a jihohin Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Yamma.
Darakta Janar na NiMet, Farfesa Mansur Bako Matazu, da Darakta Janar na Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya (NIHSA), Mista Clement Nze, ne suka bayyana hakan a wajen bude taron bita kan yanayin binciken hangen nesa da aka yi (HydroSOS).
Shugaban NiMet ya ce nan da kwanaki kadan masu zuwa, akwai yiwuwar maka ruwan sama mai karfin gaske wanda hakan zai tilasta bude madatsun ruwa na wasu dam, hakan kuma zai iya samar da ambaliyar ruwa.
Jihohin Binuwai da Kogi na fama da ambaliyar ruwa mai yawan gaske, kamar yadda aka yi a shekarar 2012.
Ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan ta janyo asarar rayuka da dukiyoyi na biliyoyin Naira a jihohin.