Alakar tattalin arziki da cinikayya bisa daidaito da aminci kuma mai dorewa tsakanin Sin da Amurka ta dace da muhimman muradun kasashen biyu, kuma za ta amfanar da kamfanoni a duk duniya, a cewar mataimakin ministan cinikayya Wang Shouwen yayin wata ganawa da Ramon Laguarta, shugaban kamfanin PepsiCo a ranar Talata.
Da yake karin haske kan yadda kasar Sin ke da karfin gwiwar cimma burinta na bunkasa tattalin arzikinta na shekarar 2025 da aka gabatar a cikin rahoton aikin gwamnati, Wang, kuma wakilin harkokin cinikayya na kasa da kasa na kasar Sin, ya bayyana cewa, wasu jerin tsare-tsare da kasar ta bullo da su na fadada bukatun cikin gida, da sa kaimi ga inganta tsare-tsaren yin sayayya za su samar da karin damammaki ga kamfanonin masu jarin waje, ciki har da PepsiCo. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)