Daga lokacin da da namija ya tara da ‘ya mace ba tare da amfani da kororon roba wanda zai ba ta kariya daga daukar ciki ba, sannan ta fara jin wasu sauye-sauye a jikinta, daga nan akwai yiwuwar samun juna biyu.
Har ila yau, akwai wasu kananan alamomi da mace za ta iya gani yayin da ta dauki ciki wadanda suka hada da:
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Zai Tattauna Da Mashawarcin Shugaban Amurka Kan Tsaro Yayin Ziyararsa A Thailand
- Kyan Alkawari Cikawa
– Yawan bacin rai mai iya haddasa kuka: Wannan yana faruwa ne sakamakon canje-canjen sinadaran ‘hormones’ da ke faruwa a lokacin da mace ta dauki ciki, wani lokaci ma mace kan iya fashewa da kuka ba tare da an yi mata laifin komai ba.
– Hakan nan, mafi yawan lokaci mace na samun matsalar kumburin ciki da zarar ta ci abinci, sannan kuma ga matsalar yawan yin tusa.
– Fitar jini dan kadan daga al’aurar mace. Wannan jini da yake fita, wasu matan kan dauka jinin al’ada ne, amma yana da bambanci matuka da na jinin al’ada; sakamakon cewa bai kai na al’ada yawa da duhu da kuma wari ba.
– A daidai wannan lokaci, mata kan samu matsalar ciwon mara; amma matsakaici
– Haka nan, su kan samu kansu a wani yanayi na yawan jin kanshi ko wari na wasu abubuwa, inda kanshin wasu abubuwan kan iya sa su kaiwa ga yin amai
– Sannan, akwai matsalar rashin jin dadin abinci ko kuma kwadayin wasu nau’o’in kalar abincin daban.
– Akwai kuma matsalar yawan toshewar hanci lokaci zuwa lokaci.
Kazalika, mai ciki na samun kanta a wani yanayi na yawan yin zazzabi ko kuma ciwon kai.
– Haka nan, batun yawan tara yawu a baki. Masu ciki da dama na haduwa da irin wannan matsala ta tara yawu a baki, wasu har sai bayan sun haihu kafin su rabu da matsalar.
– Yawan toshewar hanci, na daya daga cikin wadannan alamomi na samun juna biyu.
– Matsalar fitar kuraje a fuska, shi ma wani bangare ne da ke nuna alamun daukar ciki.
Har ila yau, da zarar kin lura da wadannan alamomi a jikinki, sai ki yi maza ki fara da yin gwajin ciki na fitsari tun a gida. Sannan, da zarar sakamakon ya nuna akwai ko babu; sai kuma ki sake garzayawa zuwa asibiti don yin gwajin jini.
Haka nan, idan sakamakon gwajin cikin jinin ya nuna akwai cikin, sai kuma a je a yi hoton ‘ultrasound’; domin tabbatar da lafiyar cikin.
A ka’idar ilimin likitanci, ana iya tabbatar da cewa mace na da ciki ne kadai, bayan an yi hoton ‘ultrasound’ an ga cikin a cikin mahaifa.