Shi dai harshe wani tsari ne ga bil adam wanda ake amfani da shi wajen isar da sako ko musayar bayanai tsakanin juna. Harshe ya kunshi sauti da rubutu a matsayin wani bangare na al’adun wata kabila. Harshen ya bambanta tsakanin wannan al’umma zuwa waccan al’umma.
Harshen Mandarin, dadadden harshe ne mai dogon tarihi da al’ummar Sinawa ke amfani da shi, ya kasance harshen da aka fi amfani da shi a duniya. Yau an wayi gari harshen Mandarin yana yaduwa cikin sauri a nahiyar Afrika. Sakamakon bunkasuwar ma’amalar cinikayya, diplomasiyya da musayar al’adu tsakanin Sin da Afirka ya sanya harshen Mandarin ya samu karbuwa a matsayin wata hanyar da za ta saukaka mu’amala da kuma zurfafa dangantaka a fannoni daban daban tsakanin al’ummomin Afirka da na Sin.
Bugu da kari harshen Mandarin abu ne mai muhimmancin gaske ga ’yan kasuwar Afirka da suke mu’amala da ’yan kasuwar Sin, abin da zai saukaka masu dawainiya da masu yi masu tafinta yayin da suke tattaunawa tsakaninsu da abokan cinikayya na kasar Sin. Harshen Mandarin ya bude damammaki ga jama’a tare da samar da aikin yi, musamman idan aka yi la’akari da yadda a kullum bukatar masu iya magana da Mandarin ke karuwa.
Har wa yau kuma, yaduwar harshen na Mandarin yana da alfanu wajen fahimtar al’adun kasar Sin, abin da zai taimaka wajen wayar da kan masu korafi kan batun ’yancin dan adam, tare da fahimtar yadda Sin ke samun bunkasuwa cikin sauri.
Idan muka duba a fannin ilimi da al’adu kuwa, kasar ta Sin ta rubanya yawan gurabun karo ilimi ga dubban dalibai daga Afirka, abin da ya sanya koyon harshen na Mandarin ya zama wajibi ga irin wadannan dalibai.
Yanzu haka dai akwai jami’o’i da kwalejoji da cibiyoyi da dama da ake koyar da harshen mandarin a kasashen Afirka. Yayin da dalibai masu koyon harshen Mandarin suke ta karuwa a kullum. Misali a kasar Uganda akwai cibiyar koyar da harshen Mandarin wadda ta fara da dalibai 30 a shekara goma da ta gabata, amma a yau tana da sama da dalibai 400.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp