Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar, sun karu da kaso 5.2 bisa dari kan mizanin shekara shekara a cikin watanni 9 na farkon bana. A cewar hukumar, a lokacin, tattalin arzikin kasar ya samu ci gaba ba tare da tangarda ba, wanda ya kai ga samun kyawawan sakamako a fannin ci gaba mai inganci.
Ta kara da cewa, cikin rubu’i na 3 na bana, GDPn ya karu da kaso 4.8 kan mizanin shekara shekara.
Haka kuma, cikin watanni 9 na farkon bana, adadin kayayyakin da Sin ta samar ya karu da kaso 6.2 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)