Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin da hadin gwiwar jami’ar Renmin, karkashin cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani suka fitar, ya nuna gamsuwar masu bayyana ra’ayoyi na sassan kasa da kasa da karfin tattalin arzikin Sin.
Alkaluman sun nuna yadda kaso 89.5 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin suka jinjinawa karfin tattalin arzikin kasar, ciki har da ’yan kasa da shekaru 44 da gamsuwarsu ta haura kaso 90 bisa dari.
Baya ga hakan, kaso 89.3 bisa dari na masu bayyana ra’ayin sun jinjinawa kasar Sin, bisa kwazonta na wanzar da ci gaban tattalin arziki. Sai kuma kaso 86.4 bisa dari da suka bayyana cikakkiyar gamsuwa da muhimmancin gudunmawar kasar Sin ga ci gaban tattalin arzikin duniya.
Alkaluman sun nuna gamsuwar kaso 95.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin daga nahiyar Afirka, da kaso 92.9 bisa dari daga yankin kudancin Amurka, da kaso 85.6 bisa dari daga nahiyar Asiya. Kuma gamsuwar masu bayyana matsaya ’yan kasa da shekaru 44 ta haura kaso 88 bisa dari.
Duk da yanayin kasa da kasa mai cike da nuna ra’ayin kashin kai da kariyar cinikayya, masu bayyana ra’ayoyin daga sassa daban daban na duniya sun gamsu da ingancin kasuwar kasar Sin, da damammakin bude kofa bisa matsayin koli da Sin din ta samar.
Wani binciken tattara ra’ayoyi da aka gudanar a shekarar nan ta 2025, ya nuna kaso 72.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun gamsu da manufar Sin ta bude kofa, da kasuwarta mai amincewa da kyakkyawar takara. Kana kaso 79.8 bisa dari na ganin babbar kasuwar Sin ta samar da muhimman damammaki ga kasashensu na asali. (Saminu Alhassan)