Gwamnatin Sin ta gabatar da alkaluman bunkasar tattalin arzikinta a farkon watanni 3 na bana a jiya Laraba, wato kaso 5.4 bisa dari. Adadin da ya bayyana ingancin tattalin arzikinta mai cike da kuzari, kuma hakan ya shaida cewa yana da cikakken karfin tinkarar duk wani kalubale daga waje. Shugaban gudanarwar asusun hadin gwiwar Amurka da Sin John Milligan-Whyte, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai na CMG.
Kafar BBC ta ba da labarin cewa, bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya zarce hasashen da aka yi a baya. Baya ga hakan, jaridun Financial Times da Bloomberg, sun bayyana halin inganci da dorewa da tattalin arzikin Sin yake ciki.
- An Watsa Shirin Bidiyon “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” Na Harshen Cambodia
- Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa
Idan an waiwayi rahoton da aka fitar game da tattalin arzikin Sin a farkon watanni 3 na bana, abin da ya fi bayyana muhimmanci shi ne inganci da karko. A cikin wadannan lokuta, alkaluman bukatun kayayyaki na karuwa cikin sauri, karuwar daraja a bangaren masana’antu ya kai kashi 6.3% bisa na makamancin lokacin bara, adadin ya kai kashi 5.3 ta fuskar ba da hidimomi, kana yawan jarin da aka zuba a manyan kadarori ya karu da kashi 4.2 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara.
Ban da wannan kuma, alkaluman PMI wato masu bayyana yanayin sayayya da ake ciki ta fuskar sana’o’in samar da kayayyaki a watan Maris ya samu karuwa cikin watanni 2 a jere, matakin da ya bayyana bukatun kasuwanni na kara samun kyautatuwa. Har ila yau, Sin ta kafa cikakken tsarin sana’o’i, da ingantattun manufofin dake da nasaba da su bayan kokarin da take yi a shekaru da dama, matakin da ya aza tubali mai inganci ga bunkasuwar tattalin arzikinta.
Bayan ga batun dorewa, Sin ta bayyana kuzarinta mai karfi a fannin samun bunkasuwa. A cikin shekarun baya-bayan nan, Sin ta sauya salon tattalin arzikinta daga matakin dogaro da zuba jari, da fitar da kaya waje, zuwa habaka bukatun cikin gida da gaggauta kirkire-kirkire tare. A shekaru 5 da suka gabata, bukatun cikin gida ya taka rawa da yawansa ya haura kashi 80 cikin dari ga bunkasuwar tattalin arzikinta. Alkaluman farkon watanni ukun bana, sun bayyana wannan sauyi da Sin take samu.
Yanayin bunkasuwar tattalin arzikin Sin mai karko da inganci a dogon lokaci ba zai canja ba duk da matsin lamba, da matakin karin harajin kwastam da Amurka ke kakabawa sauran sassa ke kawo mata a gajeren lokaci. Sin tana da kwarin gwiwa, da cikakken karfi tinkarar kalubaloli daga waje, da cimma muradunta na samun bunkasuwa bisa ingantattun manufofin gwamnatinta daga manyan fannoni. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp