Kamar yadda Allah yake fada cewa, ba shi da tamka (Laisa kamislihi shai’un…) haka ma ya alakanta azumi cewa shi ma ba shi da tamka.
Kowacce ibada yi ake yi za ka ji mutum na fadin cewa shi ya yi – na yi Sallah, na yi Sadakah, na yi…, da dai sauransu. Amma shi azumi korewa yake yi – na bar ci, na bar sha, na bar saduwa da iyali daga lokaci kaza zuwa lokaci kaza, na bar fada, na bar kaza da kaza da dai sauransu. Hadarar Allah ita ma korewa take yi – Allah ba shi da da, ba ya ci, ba ya sha, don haka ibadar azumi ce kawai ta kwaikwayi wannan Hadara ta korewa – ba ci, ba sha, ba saduwa da iyali, ba ba…
Allah Ubangiji ya alakanta azumi da kansa inda yake cewa “Assaumu li, wa ana ajzihi” azumi nawa ne, kuma ni zan saka da ladansa. Azumi ya dara wa sauran ibadu.
Idan muka duba azumi a shari’ance (ma’anar azumi kamewa) a wannan ma’ana ta azumi ma’anarsa kamewa, akwai wata hikima a kan hakan – kar mu ci, kar mu sha, kar mu sadu da iyali, shi ake nufi da Siyamu (Kutiba alaikumus siyamu). Amma azumin kar mu yi karya, kar mu yi cece-ku-ce, shi kuma sunansa Saumu – sabida fadar Mahaifiyar Annabi Isah Sayyada Maryama (AS) da Allah Yake ce mata, idan sun tambaye ki, a ina kika samo yaro? ki ce musu, ina azumi (… inni nazartu lirrahmani sauman, falan ukallimal yauma insiyya), don haka siyamu kwana 29 ne zuwa 30 amma saumu har abada ba a gama shi. Babu randa za a ce mutum ya daina halin kirki da mutunci (Saumu) amma shi siyamu shi ke kai mu ga Saumu.
Wanda ya kame daga sha’awan cikinsa da farjinsa amma bai iya hakuri da rama fada ba, bai iya yin sauran kyawawan dabi’u ba to ya yi azumi kuma azuminsa ya amsu sai dai bai samu daraja da falala ba kamar irin wanda ya hada da kame bakinsa wajen mayar da zage-zage.
Azumi ya kasu gida Hudu:
Akwai na wajibi – ya rabu kaso Uku.
1- Ya wajaba da wajabtawar Ubangiji ba don wani laifi ba, shi ne azumin watan Ramadana, sai dai ya ce mana, ya wajabta mana ne don mu yi Takwa (…Kutiba alaikumus siyamu kama kutiba alallazina min kablikum, la’allakum tattakun) Allah ne cikin rahamarsa ya wajabta mana ba don wani ya yi wani laifi ba sai don yana son ya bude wata kofa ta alkairi a gare mu.
2- Akwai wanda ya wajaba sabida wani abu da ya wajabta shi, shi ne azumin Kaffara. Idan mutum ya kashe wani mutum ba da gangan ba, dangin mamacin suka ce sun yafe, sannan hukuma ta ce ta yafe, to shi Ubangiji bai yafe ba sai ka yi kaffarar azumi 60 a jere. in mutum ya sadu da iyalinshi a watan Ramadana, to sai mutum ya yi azumin kaffara 60 a jere, da zai yi 59 sai ya sha na karshe, sai ya sake. Wannan Kaffara wajibi ce amma wani abu ne ya wajabta ta.
3- Akwai wanda yake wajabta sabida Dan Adam da kansa ya wajabta ma kansa, shi ne azumin ba-kance. Mutum ya ce, Ya Ubangiji in ka biya min bukata ta kaza, ni kuma na yi alkawarin yin azumi kaza, yanzu wannan azumin kai ka dora wa kanka kuma ya zama wajibi in bukatarka ta biya, Allah ya yabe su a cikin ayar (Yuufuna bin nazri wa yakhafuna yauman kana sharruhu mustadira ).
Akwai na Nafila: azumin da an so ka yi don neman lada.
Shi wannan azumi, na wani lokaci ya fi na wani lokaci kamar an so a dinga yin azumi sau Uku a cikin kowanne wata, lokacin kwanan wata yana 13 da 14 da 15, wannan kwanaki hasken wata ya fi haske a cikinsu, to kamar yadda suke haske haka zuciyarka za ta kara haske sabida saduwa da hasken, sannan kuma hawa-hawa na musulunci guda Uku ne (Islam da Iman da Ihsan) to wanda ya riski wannan kwanaki Uku kamar Ya hau dukka wannan Matakan addinin ne.
Akwai azumin Litinin da Alhamis, azumin ranar Litinin Annabi ((SAW)) ne yake yi, an tambaye shi cewa Ya Rasulullahi sabida me kake azumin ranar Litinin? sai ya ce ranar ce aka haife ni, ina godiya ga Allah. To duk wanda ya yi azumin ranar Litinin ya yi koyi da Annabi ((SAW)) ne. Azumin ranar Alhamis kuma, Annabi ((SAW)) ya ce ranar ake nade ayyukan bayi na mako zuwa ga Ubangijinsu Rabbul Izzati, ina kwadayin a kai aikina ga Ubangiji ina azumi. Akwai sauran azumomin nafila da yawa.
Akwai babban azumin nafila da ake cewa ‘Na Annabi Dawudu’: Annabi Dawudu Mutum ne sarki mai ibada, yana daga cikin Ibadarsa azumi. In ya yi azumi yau, gobe sai ya ci abinci, haka ya kasance yanayi a rayuwarsa, idan ya rayu shekaru 60 – shekaru 30 ya yi azumi.
Allah yana gode wa Dan’adam in ya ce zai yi azumi duk ranar da yake so sai dai ba a so ya ware wata rana kamar Jumu’a ko Asabar ya dinga azumtarsu duk sati. Lallai azumi yana da falala sosai.
Allah ya wajabta mana azumi kamar yadda ya wajabta ma wadanda suka zo kafin mu.
An karba hadisi daga Mu’azu bin Jabal yana cewa: “Manzon Allah (SAW) bayan ya yi Hijira zuwa Madina, sai wata rana, Yahudawan Madina duka suka tashi da Azumi – Ashura, sai Annabi (SAW) Ya tambayesu lafiya, sai suka ba shi amsa da cewa ai wanna ranar ce Allah ya tseratar da Annabi Musa ya hallakar da Fir’auna, sai Annabi (SAW) yabce mu muka fi cancanta da Musa”. Annabi (SAW) ya yi umarnin cewa kowa ya ci gaba da azumin, shekara mai zuwa Allah ya saukar da azumin watan Ramadana, Annabi (SAW) ya ce Allah ya ba mu namu wanda ya so ya ci gaba da na Ashura, har Annabi (SAW) ya koma ga Allah yana azumin Ashura, azumin yana daga cikin manyan azumin Nafila a addinin Musulunci.
Ya zo cewa Annabi (SAW) ba ya barin azumin kwana Uku na kowanne wata. Idan mutum yana yin azumin kwana Uku na kowanne wata za a rubuta masa ladan kwana 30, sabida kowanne aiki daya ana rubuta masa goma, don haka azumin kwana uku dai-dai yake da uku sau Goma, Talatin kenan.
Allah ya wajabta azumin Watan Ramadana ga al’ummar musulmi bakidaya, amma a farko masu hali (dukiya) ciyarwa suke, marasa dama kuma su yi azumi, har sai da Allah yace “Wa’anta sumu khairullakum” sannan ya zama wajibi a kan kowa. Amma har gobe, yana nan marasa lafiya su kididdige kwanukan da suka tsere musu su biya a wasu ranaku bayan watan Ramadana, wadanda ba za su iya azumtar watan ba su ciyar, matafiyi in ba zai iya azumi cikin tafiyar ba, shi ma ya ciyar.
Yana daga cikin falalar watan Ramadana, Annabi (SAW) ya ce idan Watan Ramadana ya zo, duk kofofin Aljannah bude su ake yi, duk kofofin wuta kuma sai a kulle, kuma sai a kulle duk shaidanu, sai ka ga masallatai duk sun cika, sabida abokin yawon shaidancin an kulle shi. Ba ana nufin Aljannu da suke kama mutane ba na rashin lafiya, wannan ciwo ne, lada za a bai wa majinyacin, abokin yawon shaidancin ake daurewa.
Nasa’i ya ruwaito cewa kullum mai kira zai yi kira a cikin dare, yana cewa “ya kai mai neman alheri taho, ga watan alheri ya zo, ya kai mai neman sharri kame, wannan ba watan sharri ba ne.”
Wasu daga cikin Malamai sun tafi cewa ‘Ramadana’ sunan Allah ne sabida Hadisin Abi Hurairah da yake cewa “kar ku ce Ramadana ya zo, sabida Ramadana suna ne daga cikin sunayen Allah”. Allah a Littafinsa cewa ya yi “Shahru Ramadana…” Amma ba laifi in an ce Ramadana ya zo sabida ana nufin watan Ramadana.
Allah ya saukar da mafificin littafi (Alkur’ani) a cikin watan Ramadana, a mafificin dare (Lailatul Kadri).
An karba daga Abdullahi bin Abbas, Allah ya yarda da su, yake cewa “Allah Ya saukar da Alkur’ani daga lauhil mahfuzi izuwa saman Duniya (a cikin Ramadana aka saukar da alkur’ani daga lauhil mahfuzi zuwa saman Duniya, a dakin Baitul ilimi), Mala’ika Jibril (AS) shi kuma daga nan yake debo ayoyinsa zuwa ga Annabi (SAW), sai da ya shafe shekaru 23 yana kan wannan aikin.