• English
  • Business News
Friday, October 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
7 hours ago
Allah

Masu karatu assalamu alaikum wa rahmtullah. Barkanmu da sake saduwa a a ci gaba da darasinmu a wannan shafi na Dausayin Musulunci mai albarka. Har yanzu dai muna nan a cikin yabon da masanin falsafan nan ya yi wa Manzon Allah (SAW) wanda shi ilimi ne ya bi, ba ma addini ba.

Allah (SWT) ya daukaka matsayin Manzon Allah (SAW) a cikin dukkan komai. Kamar yadda darasinmu na makon da ya gabata ya yi matashiya. Manzon Allah (SAW) ya taba tambayar Jibril (A.S.) me ake nufi da “Wa rafa’ana laka zikirak”sai Jibri (A.S.) ya ce ya tambayo masa, sai ya ce abin da ake nufi shi ne duk lokacin da aka ambaci sunan Allah sai an ambace ka cikin Sallah da cikin ambatonsa da sauransu, saboda (Manzon Allah) ya kare cikin Halarar Allah, saboda matsayin da ya kai (S.A.W).

  • Mauludi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Juma’a A Matsayin Hutu
  • Zan Ci Gaba da Taka Leda A Kano Pillars Duk da Matsayin Da Na Samu — Ahmed Musa

Imamu Zuhuri, (malamin hadisi ne), yana cikn salafus salihin, yake cewa da mutum zai yanka saniya ko ya yanka rago ko kaza da sunan Manzon Allah (S.A.W.) ya halatta a ci, saboda me, saboda Ubangiji ya ce “Wa rafa’ana laka zikirak” ya kawo ambatonsa a wajen, amma in da irin shuwagabanninmu ne na nan sai su ce Haram. Amma sun ce da kirista zai iya yin yanka musulmi ya ci, Allah ya ce abincinsu halal ne a wajenmu, mu ma namu halal ne a wurinsu, sai dai ban da giya da alade da Allah ya haramta (don babu wani abinci na alade da za a kawo ka ci), ka ga bambancin karatun malamai na baya da na yanzu, na baya suna da zurfin tunani.

Malami Masani Bafalasafen ya ci gaba da cewa, Allah ya kai Manzon Allah mukamin mahmudi (shi ne mukami na yabo a cikin komai). Shi Manzon Allah a cikin komai halin yabo ne da shi, komai nasa abin yabo ne don haka ake cewa Muhammadu sha yabo (S.A.W.), komai na Allah yabo ne ga Allah saboda haka komai suna gode wa Allah, wani abin za ka fahimta wani abin kuma ya fi karfin ka fahimta, kamar ka ga baban wani ya jika madaci yana ba yaronsa ba wai ba ya son sa ba ne, idan ka ga likita ya yanka cikin mutm don ya yi magani (tiya) ne ba don ya kashe shi ba, idan ka ga malami ya daki yaro ba don ba ya son sa ba ne don ya daina wasa ne ya yi karatu, amma kuma kar kana malami ka ji haka ka je ka yi ma yaro dukan hauka.

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (1)

LABARAI MASU NASABA

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Idan ka duba tarihin duniya gabadaya da tarihin annabawa, tarihi ne na wayewar duniya tun daga Annabi Nuhu (S.A.) har zuwa Manzon Allah (S.A.W.) kamar duniya tana ‘yar makaranta ce ta fara da Nazare, ta zo Firamare zuwa Sakandire har zuwa Jami’a, sannan aka yaye ta, yanzu da zuwan Manzon Allah an yaye duniya, yanzu duniya ba ta bukatar sai an aiko annabi, ba ta bukata sai an aiko ma’aiki, a’a wanna abu da Manzon Allah ya zo da shi za mu iya kafa dalili da shi mu shirya kanmu ba sai da annabi ba.

Wannan abu da Manzon Allah ya zo da shi yanzu ya kafa dalili da shi, da shi muka karantar da kanmu ba sai da Annabi ba, wannan abu da ya zo da shi za mu iya aiki da shi mu zauna lafiya, mu haramta abin da Allah Ya haramta. Yanzu kamar an yaye mu ne daga Jami’a tun daga jami’a tun daga zamanin Annabi Nuhu (A.S.) har ya zuwa Annabi Muhammadu (S.A.W.). idan ka faro duniya daga farkon ma’aika, duniya ta faro ne daga sanin wuta wato yadda za a yi amfani da wuta. Dan adam na farko ya ji tsoron wuta wasu sun tafi a kan cewa farkon abin da Dan Adam ya fara bautawa shine wuta, wanda ita ta fara ba shi tsoro ba wai ya iya kunnawa ba amma ya ga daki ya kama da wuta, dubi irin zamanin nan duk da motocin kashe gobara haka daji zai kama da wuta ta gagare su balle ka koma zamani da shekara miliyan kaza wanda dan Adam bai ma santa ba sai dai ya ga daki ya kama da wuta (wata ay ana cewa) “Allahn da ya sa muku wuta a ciki koren ganye ko koriyar bishiya”, malamai na cewa bishiya mai yado wanda ake kunna wuta, toh wannan abu ne ya sa idan wuta ta kama aka kasa shawo kanta sai mutane su tsorata su ce wai meye wannan, meye ya kunna wannan wutar? Suka ga to lallai wannan duniyar da suke ciki akwai wani abu a boye, gwara su bauta wa abin nan na boye fa, don ya kiyaye su daga wanna wutar har suka fara bauta mata da yanka dabbbobi don ta kiyaye su, gaba daya dai har ta soma gasa wasu abubuwa na dabbobi, idan wutar ta mutu suka zo wurin su ji kamshin ya bambanta, idan sun sa a baki su ji dadinsu ya banbanta. Toh tana daya daga cikin abin da ta koya wa dan Adam wayewa.

Da dan Adam ya waye, wuta tana daya daga cikin abin da ya wayar da dan Adam kuma idan ka lura yau wuta ita ke biye da mu duk wasu kere-kere za ka ga daga wuta ne, abin da muke tsoro kuma shi ne babban abin amfani, toh a haka dai dan Adam har ya iya kera wutar da kansa. Kamar yadda Allah ya fada mana cikin ‘ya’yan Adam da daya ya kashe daya ya rasa yadda zai yi, a haka ne har dan Adam ya san yadda zai binne dan’uwansa har zuwa zamanin Annabi Idirisu sama ta soma magana da kasa, Allah ya soma aiko ma dan Adam da mala’ika, su ne wadannan mutane da muke cewa ko akwai su a duniyar wata ko mutanen sama, Turawa duk sun rubuta wannan abu, sun zana wannan abu sai ga shi irin wannan jirage ne wanda ake cewa na duniyar sama, daya daga ciki Annabi Sha’ayahu yake cewa ga wani abu ya sauko kasa mai kara iri kaza.

Tun daga zamanin Annabi Idris mala’iku ne suka kawo sako suke yin magana da mutanen kasa, su ake cewa tatsuniyoyi na duk al’umma, tatsuniya ne a wajenmu amma su gaske ne a wajensu, su ce mutane sun sauko musu daga sama, har aka zo zamanin Annabi Nuhu ya tabbatar, da ya zo ya fada wa mutane suka ce ba su yarda ba, ba mu ji wannan wajen iyayenmu ba, haka aka ci gaba har zuwa zamanin Annabi Hudu dan Adam ya fara hore dabbobi, dabbar da dan Adam ya fara horewa shi ne kare, kuma ya hore dabbobin da zai ci, zai iya gane wannan dabbar ba zai ci ba wannan zai ci, wannan zai iya zama da ita lafiya, wannan ba zai iya zama da ita ba, daga nan dan Adam ya fara gini, ya dan kwakule kasa ya yi kogo ya shiga.

Har ya zuwa Annabi Salihu, har dan Adam ya fara fahimtar wannan kwayar da take fitowa a kasa, wannan zan iya ci in rayu, wannan kwayar kuma ba a cin ta, har ya soma tunanin toh wannan kwayar ya zan ajiye ta zuwa nan gaba in sake shuka ta, haka dan Adam har ya soma yin noma a aikace don ya rayu. Allah ya gaya mana wannan yana daga cikin ayoyin Allah (kamar yadda ya zo a aya) “arziki yana daga cikin kasa da abin da kasa take tsirarwa da abin da hannunka yake aikatawa” kamar sana’a ko noma ko nema. Toh ka ga a nan babu zancen ka ce ba za ka yi nema ba, duk abin da kake nema idan ka juya kasa za ka same shi, duka kasar da ta rike noma da sana’a za ku ga sun fi arziki, Allah ga shi ya gaya mana idan kafiri ya fi ka arziki sai dai ka nema a wajensa, don haka mu dogara da Allah shi ke azurtawa, ga ka’idoji nan ya fada mana, nema, kiwo abubuwa duk gabaki daya.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa in sha Allahu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
Manyan Labarai

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Manyan Labarai

NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa

October 31, 2025
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi
Manyan Labarai

Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

October 31, 2025
Next Post
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

LABARAI MASU NASABA

Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede

Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede

October 31, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida

October 31, 2025
Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

October 31, 2025
Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa

October 31, 2025

Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda

October 31, 2025
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai

October 31, 2025
Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.