Allah ya yi wa Sarkin Dutse rasuwa na birnin jihar Jigawa, Alhaji Nuhu muhammadu Sunusi II, kamar yadda gidan talabijin din Channel ta nakalto.
Sarkin mai daraja ta daya a arewa maso yammacin Nijeriya, shi ne tsohon shugaban jami’ar jihar Sokoto.
Alhaji Mustafa Sule Lamido, wanda ke rike da sarautar Santurakin Dutse kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jigawa, ya wallafa rasuwar Sarkin a shafinsa na Facebook cikin alhini da jimami.
Kazalika, wata majiya mai tushe ta shaida cewar sarkin ya rasu ne a ranar Talata a Abuja amma ba a shaida wurin da ya rasun ba zuwa yanzu.
Shi dai Alhaji Nuhu Muhammadu Sunusi ya zama sarkin Dutse ne bayan da gwamnatin soji a karkashin marigayi Kanal Ibrahim Aliyu ta nadashi a shekarar 1995 bayan rasuwar mahaifinsa Muhammadu Sunisu.
Alhaji Nuhu ya shafe tsawon shekara 28 a karagar masarautar Dutse da ke da dumbin tarihi a cikin masarautun arewa.
Cikakken labari na tafe..