Kwanan nan ne wasu kafafen yada labaran kasashen yammacin duniya, suka kwatanta alluran riga-kafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar, da wadanda sauran kasashe suka samar, ciki har da na kamfanin Pfizer, inda a cewarsu, wai alluran riga-kafin kasar Sin ba su taka rawar gani ba.
Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Jumma’a cewa, shaidu sun tabbatar da cewa, alluran riga-kafin kasar Sin na da tsaro da inganci.
Wang ya ce, kwanan nan manyan jami’an hukumar WHO sun bayyana cewa, mutane masu tarin yawa sun karbi alluran riga-kafin cutar COVID-19 a kasar Sin, kuma komai nau’insa, na da makamancin amfani ga riga-kafin alamomin cutar masu tsanani gami da mutuwa.
Wang ya kuma kara da cewa, binciken ya shaida cewa, ga mutane masu shekaru sama da 60, amfanin karbar alluran riga-kafin kasar Sin sau uku, da amfanin karbar alluran riga-kafin kamfanin Pfizer nau’in mRNA sau uku, a fannin kiyaye mutane daga mutuwa, ko kamuwa da cuta mai tsanani, kusan iri daya ne. Alluran riga-kafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar, suna taka muhimmiyar rawa, wajen riga-kafin kamuwa da cutar, da kuma kare mutane daga kamuwa da cutar mai tsanani ko kuma mutuwa. (Murtala Zhang)