Sakamakon wani nazarin jin ra’ayin jama’ar nahiyar Afrika ya nuna cewa, kaso 90.4 na wadanda suka shiga nazarin, sun yi ammana cewa ka’idoji da matakan hadin gwiwar Sin da Afrika sun zama abun misali ga kasashe masu tasowa, ta fuskar dangantakar kasa da kasa, kuma sun samar da muhimmiyar mafita wajen yi wa tsarin tafiyar da harkokin duniya garambawul.
Kafar yada labarai ta CGTN da jami’ar Renmin ta kasar Sin ne suka gudanar da nazarin ta hannun cibiyar tuntubar kasa da kasa a sabon zamani domin masu bayar da amsa daga nahiyar Afrika.
- Wang Yi Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Ta Hanyar Gudanar Da Taron FOCAC
- Da Yiwuwar A Rage Wa Ƴan Majalisa Albashi
Kasancewar daya, kasa mai tasowa mafi girma a duniya, dayan kuma nahiya mafi yawan kasashe masu tasowa, kamanceceniya ta fuskar tarihi da burin ci gaba ya sa kasashen Sin da na Afrika zama abokai na kut da kut kuma abokan hulda, kana ’yan uwa masu kasancewa da juna komai wuya, komai dadi.
Mutane 10,125 daga kasashen Afrika 10 ne suka bayyana ra’ayoyinsu cikin nazarin. Kasashen sun hada da Kamaru da Botswana da Masar da Habasha da Ghana da Kenya da Morocco da Nijeriya da Afrika ta Kudu da kuma Tanzania. (Fa’iza Mustapha)