• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Al’ummar Kasashen Turai Na Dandana Kudar Rikicin Rasha Da Ukraine

byCMG Hausa
3 years ago
Turai

Yau kusan watanni shida ke nan, tun bayan barkewar rikici a tsakanin Rasha da Ukraine. Sakamakon rikicin, kamfanonin samar da makamai da na hatsi na Amurka sun ci kazamar riba, a yayin da kamfanonin samar da makamashi ma ba su so a bar su a baya. 

Bayanai na nuna cewa, sakamakon yadda kasashen Turai suka biyewa kasar Amurka wajen kakaba takunkumai kan Rasha, yanzu haka, kasashen Turai da dama na fuskantar matsalar karancin makamashi mai muni, hakan ya tilasta musu sayen iskar gas daga wajen Amurka a kan farashi mai tsada, matakin da ya sa kamfanonin samar da makamashi na kasar Amurka cin kazamar riba, inda kusan kowane jirgin dakon iskar gas na kamfanonin Amurka da ke zuwa Turai, na iya cin kazamar ribar da ta kai dala miliyan 100.

  • Ma’aikatan Gwamnati Sun Fi ‘Yan Siyasa Cin Hanci Da Rashawa – Kwamitin Majalisar Dattawa

Abin takaici shi ne, a yayin da ake fuskantar hauhawar farashin wutar lantarki da yadda aka kayyade wutar da ake samar musu, al’ummar kasashen Turai su ne suke dandana kudar rikicin.

Kwanan nan ne, zanga zanga ta barke a birnin Prague, babban birnin kasar Czech, inda kimanin mutane dubu 70 suka bazama kan tituna suna kira ga gwamnati da ta dauki matakai na shawo kan saurin hauhawar farashin makamashi, tare da sukan gwamnati a kan manufarta ta yin biyayya ga kasashen yammaci wadda ta illata moriyar kasar.

Kwanan baya, shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya sake sanar da samar da gudummawar soji da za ta kai darajar kusan dala biliyan 3 ga kasar Ukraine.

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Kafin wannan, Amurkar ta samar da gudummawar soji a kalla dala biliyan 10.6 ga Ukraine. Kamar yadda tsohon dan majalisar dokokin kasar Burtaniya, George Galloway ya fada ne, “Kamar dai yadda Amurka ke son ganin Ukraine ta yi ta yaki har sai a karshe ta fadi kasa warwas, haka ta shirya ganin durkushewar Turai.”

Amurka dai ta tada rikicin tsakanin Rasha da Ukraine, ta kuma rika rura wutar rikicin, amma ta koma gyefe tana cin riba a fakaice. Nan ba da dadewa ba, za a shiga lokacin hunturu a Turai, amma ko kasashen Turai za su ci gaba da dandana kudar sakamakon rikicin? (Mai Zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
Daga Birnin Sin

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Next Post
Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Zababben Shugaban Kenya

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Zababben Shugaban Kenya

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version