Daruruwan al’ummar Nijar mazauna Kano a karshen makon d ya gabata ne sua gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin amincewarsu da juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar tare da yin kira da a mayar da shugaban kasar, Mohamed Bazoum, kan mukaminsa.
‘Yan Nijar din sun gudanar da zanga-zangar a karamar hukumar Fagge, sun kuma yi tir da juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya yi barazana ga mulkin dimokradiyya a kasarsu.
- Hambararriyar Gwamnatin Bazoum Ta Nemi Faransa Ta Kwace Mulki Daga Sojojin Nijar
- ECOWAS Ta Gargadi Sojin Nijar A Kan Hukunta Bazoum
Lawalli Mamman-Barma, jagoran zanga-zangar ya bukaci gwamnatin mulkin soja da ta saki Bazoum da iyalansa da duk wadanda ake zargin suna da hannu ciki ba tare da gindaya wani sharadi ba.
“Muna kira da a dawo da mulkin dimokuradiyya na Shugaba Mohamed Bazoum ta hanyar lumana da sulhu da kungiyar ECOWAS.
“Al’ummar Nijar ne suka zabe Bazoum kan doka,” in ji Barma.
Ya kuma roki kungiyar ECOWAS da ta yi watsi da matakin tura sojoji Nijar, yana mai jaddada cewa tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa wajen warware rikicin.
Burma ya yabawa Bazoum bisa kokarinsa na bunkasa rayuwar mutanen Nijar, inda ya bayyana cewa ‘yan Nijar sun shaida ci gaban siyasa da tattalin arziki da zamantakewa a karkashin mulkinsa.
Barma ya kara da cewa, “Ya kamata a ko da yaushe mu tuna cewa kafin tsoma bakin sojoji a jamhuriyar Nijar, kasar a karkashin shugaba Bazoum ta samu zaman lafiya da kuma ci gaban tattalin arziki da siyasa.”