Tsohon Ministan Sufuri kuma jigo a jam’iyyar APC a Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, bai fito ya bayyana ba a taron yakin neman zaben shugaban kasa da dan takarar jam’iyyarsu ta APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi ba a Fatakwal a yammacin ranar Laraba ba.
Amaechi shi ne ya zo na biyu a zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a watan Yuni, 2022, inda ya bi bayan Tinubu, wanda ya yi nasarar lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
- Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Wa Da El-rufai Martani Kan Zargin Yi Wa Tunibu Zagon Kasa
- Aisha Buhari Ta Goyi Bayan El-rufai Kan Zargin Yi Wa Tunibu Zagon Kasa A Fadar Shugaban Kasa
Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin rashin zuwan Amaechi ba wajen gangamin yakin neman zaben da ake gudanarwa a yanzu haka ba a filin wasa na Yakubu Gowon da ke cikin garin Lambu.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Tonye Cole, jigo a jam’iyyar a shiyyar Kudu maso Kudu, Victor Giadom, da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ne suka gabatar da jawabai a wurin taron.