Abun mamaki baya karewa, a ranar 26 ga watan Oktoba ne a garin shanga da ke jihar Kebbi, wata Amarya mai suna Sadiya, ta bijire ta ce, tafasa auren Angonta saboda ya ce, ba shi da damar siya mata waya ta Naira 150,000.
Wakilinmu Abubakar Sadeeq Shanga, ya ruwaito cewa, Jama’a sun hallara ɗaurin aure kwatsam sai ga labarin amaryar ta fasa auren Saboda Ango yaki ya siya mata waya babba ta kusan kimanin Naira 150,000.
- Shin Ahmed Musa Zai Iya Dawowa Da Rigarsa A Super Eagles Kuwa?
- NNPP Ta Lashe Kujerun Shugabannin Kananan Hukumomi 44 Da Kansiloli 484 Na Jihar Kano
Kafin Aure, al’ummar karamar hukumar mulki ta Shanga sun shimfida dokar cewa, ya zama wajibi sai anyi awo na gwajin jini ga duk masu shirin Aure kafin a daura aure domin tabbatar da lafiyar ko wannensu.
Amaryar ta yi amfani da wannan damar ce, ta cewa, ba za ta je awon ba sai angon ya saya mata waya ta naira dubu ɗari da hamsin(150k) shi kuma ba shi da halin sayen, kawai sai amaryar ta yanke hukuncin idan babu wayar ita ta fasa auren kuma haka ta faru.
Da yake shi Allah a koda yaushe mai adalci ne ga bayin sa, nan take cikin ƙawayen amaryar, wata tace, idan shi angon ya amince, ta yarda a ɗaura auren da ita, abinda zai baku mamaki shi ne, ita ƙawar amaryar sunan su daya da amaryar wato (SADIYA), Alhamdulillah cikin yardar Allah da ikon sa yan’uwan ƙawar amaryar duk sun yarda sun amince kuma an ɗaura auren.
Daga gefen gidan angon kuma, Uwar marayun shanga, Hajiya Saudatu Abdullahi Shanga, uwa ga ango ta ɗauke ma Iyayen Amaryar nauyin kayan ɗaki gaba ɗaya kuma taba amaryar kuɗi Naira nubu hamsin (50k) idan taje gidan mijinta ta nemi sana’a domin ta taimakama mijinta.