Gidauniyar Tunawa da Sardauna da ke Kaduna, ta bayar da gudummawa naira miliyan 20 don tallafawa waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri
Darakta Janar na gidauniyar Injiniya Abubakar Gambo Umar, ne ya sanar da bayar da gudummawar cikin wata sanarwar da ya fitar ga manema labarai a Kaduna inda ya bayyana cewa gidauniyar ta miƙa wa gwamnan Borno Umara Babagana Zulum, yayin ziyarar jaje da suka kai masa a jiya litinin don nuna alhinnsu ga da faruwar iftila’in.
- Aikin Matatar Mai Na Ya Hana Ni Sayen Arsenal A 2020 – Dangote
- Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Bukatar Tsige Ganduje Daga Shugabancin APC
Daraktan gidauniyar ya ƙara da cewa dalilinsu na bayar da gudummawar shi ne su ragewa waɗanda iftila’in ta shafa raɗadin irin asarar da suka tafka.
Gidauniyar ta buƙaci hukumomi da shugabanni a Nijeriya, da ƙasashen waje da su tallafawa waɗanda iftila’in ambaliyar ta shafa don rage musu raɗiɗin asarar da suka tafka ya na mai cewa gidauniyar ta na yi musu addu’oi tare da fatan ubangiji ya kare faruwar makamancin lamarin nan gaba.