Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ta shawarci masu ababen hawa da matafiya da ke bi ta jihar Kogi da su kauracewa hanyar Koto-Karfe dake jihar Kogi.
Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar, Stephen Dawulung ne ya bayar da wannan shawarar a wata hira da manema labarai kan halin da babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja ke ciki.
Ya bayyana cewa, katafaren ‘go-slow’ da ake fama dashi a kusa da Koto-Karfe a karamar hukumar Kogi ta jihar Kogi akan hanyar Abuja zuwa Lokoja, na faruwa ne sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye jihar a ‘yan kwanakin nan.
Ya ba da shawarar cewa, matafiya da masu ababen hawa su yi amfani da hanyar Enugu-Ankpa-Ajaokuta-Lafia da Abuja-Minna-Mokwa-Jebba-Ilorin domin tafiya ko wanne sassan kasar nan.