Gwamnatin jihar Taraba ta umurci mazauna jihar da ke zaune a gabar kogin Benuwe da su bar yankin zuwa wuraren da ba a tsammanin fuskantar ambaliyar ruwa.
Umurnin ya biyo bayan sanarwar da mahukuntan madatsar ruwa ta Lagdo daga jamhuriyar Kamaru suka bayar cewa, masu kula da madatsar ruwan sun fara sakin ruwa daga madatsar saboda cikewa da ta yi.
- Har Yanzu Kuɗin Taimakon Ambaliya Da Borno Ta Samu A Hannunta Bai Kai Biliyan 5 Ba
- Ƴan Ta’adda Sun Lalata Wutar Lantarkin Maiduguri Zuwa Damaturu
Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a ta jihar, Hon. Zainab Jalingo wadda ta mika wa LEADERSHIP a ranar Litinin ta fitar, ta yi kira ga jama’a, musamman mazauna yankin kwarin Benuwe da su gaggauta barin yankin.
Jalingo ta bayyana cewa, Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya (NIHSA), bata yi kasa a gwiwa ba wajen fadakar da mazauna gabar kogin da su Kaurace wa yankin bayan fitar da sanarwar daga mahukunta madatsar ruwa ta Lagdo.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, ambaliyar ruwan a kogin Benuwe, tuni ta fara barazana ga manoman Karim-Lamido, inda gonaki, musamman gonakin shinkafa suka nutse a cikin ruwa.