Ambaliyar ruwa a garin Sakuwa dake karamar hukumar Katagum ta jihar Bauchi ta yi sanadiyar mutuwar mutane akalla uku tare da lalata gidaje sama da 1,400.
LEADERSHIP ta samu labarin cewa gonakin da ba a iya tantance adadinsu ba sun nutse inda hakan ke barazana ga yanayin samar da abinci ga mazauna yankin Katagum da Bauchi da sauran jihohin da ke makwabtaka da jihar Bauchi.
Gine-ginen jama’a kamar matsugunai da makarantu da wuraren wasan yara duk ruwa ya bi takansu.
Baya ga haka, gadoji da suka hada yankuna duk sun dulmiye wanda hakan ya tilastawa mazauna wuraren da abin ya shafa yin amfani da kwale-kwale don tsallakawa daga wannan yankin zuwa wancan.
LEADERSHIP ta tattaro cewa bangarori shida na hanyar da ta hada kananan hukumomin Zaki da Gamawa na jihar zuwa jihohin Jigawa, Kano da Yobe ne ambaliyar ta shafa.
Da yake jawabi a garin Sakuwa a ranar Asabar, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Abdulkadir, ya koka da irin wahalhalun da lamarin ya jefa al’ummar yankin, inda ya dora alhakin wannan bala’in da ruwan da ke kwararowa daga jihohin da ke makwabtaka da su.